Babban magana: Wata matashiya ta garzaya wata kotun Najeriya don neman izinin auren mace 'yar uwarta
- Wasu iyaye a Najeriya sunyi hannun riga na har abada da diyarsu bayan sun gano tana son ta auri wata 'yar uwarta mace
- Matshiyar da iyayenta suka sallamata ta garzaya wata kotu inda ta bukaci a daura mata aure da wata 'yar uwarta mace
- Kotun ta ki amincewa da wannan bukatar kuma iyayenta sun sanar a jarida cewa sun sallamata har abada
Duk da cewa dokokin Najeriya sun haramta aure tsakanin jinsi iri daya, masoya da dama na jinsi iri daya sukan fito fili su bayyana wa jama'a cewa suna soyaya sai dai ba kasafai ake samun wanda suka tunkarar kotu don daura musu aure ba.
Wata matashiya mai suna Shalom Shoremi yar asalin jihar Ogun ta hadu da fushin iyayenta inda har suka sallamata ga duniya bayan sun gano ta tafi wata kotun tarayya inda ta bukaci a daura mata aure da wata macen.
KU KARANTA: Wata mace ta kwancewa mijinta zani a kotu, ta kuma bukaci a raba aurensu
Iyayenta da sauran 'yan uwanta sunyi tir da abinda ta aikata har ma sun sanar da cewa sun sallamata har abada a shafukan jaridu na kasa.
Kamar yadda sanarwar jaridar ta bayyana, kotun ta ki amincewa da bukatar matashiyar saboda ya ci karo da dokar hana auren jinsi guda na 2014, wanda ya yi bayani karara cewa laifi ne yin auren jinsi a dokar Najeriya.
Dokar kuma ta akwai hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 14 ga wadanda aka samu suna soyaya tsakanin jinsi iri daya.
Bayan bayyana cewa sun sallamata ga duniya, iyayen Shallom sun kara da cewa sun haramta mata cin gadonsu har abada.
A wata labarin, Legit.ng ta ruwaito cewa Prime Ministan kasar Ingila, Theresa May ta yi kira ga Najeriya ta janye dokar hana auren jinsi guda. Ta kuma mika irin wannan rokon ga sauran kasashen da Ingila ta raina.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng