An gano wata babbar tashar Mota a Kano da masu sayar da kwayoyi ke cin Karen su babu babbaka
Mutanen yankin unguwannin dake makwabtaka da babbar tashar mota ta ‘Yankaba a kan titin zuwa Hadejia a birnin Kano sun koka a kan yadda masu sayar da miyagun kwayoyi suka mayar da tasahar cibiyar su ta cinikayya.
Aljahji Iliyasu Ayuba ‘Yankaba, shugaban tashar motar, ya bayyana takaicin sa a kan abinda ya kira rashin kishin kai da kuma na kasa da wasu matasa ke nunawa ta hanyar sayar da miyagun kwayoyi domin gurbata tarbiyar ‘yan uwan su tare da yin kira ga irin wadannan matasa das u nemi sana’a ta halak malak. Kazalika ya yi kira ga hukuma da ta kawo masu agaji domin magance wannan babbar matsala da tashar ke fuskanta.
Shugaban hukumar yaki das ha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar kano, malam Hamza Umar, y ace hukumar sa zata dauki mataki domin ba zata bar dillalai da masu amfani da miyagun kwayoyin suke cin Karen su babbu babbaka ba tare da bayyana cewar hukumar na daukan matakai a kan masu ta’ammali da miyagun kwayoyin muddin ta samu rahoto.
Kasuwar ‘Yankaba babbar kasuwa ce da tayi suna wajen cinikayyar kayan miya da kayan marmari a cikin birnin Kano.
DUBA WANNAN: Likafa ta cigaba: Magu ya samu wani babban mukami a nahiyar Afrika
A kwankin baya ne gwamnatin Najeriya ta saka dokar hana sarrafa maganin tari mai sinadarin kodin bayan wani rahoton kafar watsa labarai a kan yadda matasa ke haukacewa a Kano saboda ta’ammali da maganin tari mai sinadarin kodin.
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu sanusi II, ya taba bayyana cewar, a kalla kwalbar kodin miliyan biyu zuwa uku ake shanyewa kullum a tsakanin jihohin Kano da Jigawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng