Yadda zaka kare kanka daga wasu cututuka 6 da ke adabar mutane lokacin damina
Allah ya kawo mu lokacin damina na wannan shekarar, galibin magudanun ruwa sun toshe saboda rashin kwashe su da ba'ayi kuma ciyayi sun fara tsira a harabar gidajen mutane.
Lokacin damina dai yanayi ne da wasu cututukan da kan iya yaduwa tsakanin mutane suka fi yin tasiri misali zazabin cizon sauro, mura, Amai da gudawa da sauransu kuma galibi kananan yara ne sukafi kamuwa da wadandan cututuka.
Cikin cututukan da sukafi adabar mutane a damina zamu lissafa guda shida tare da yadda za'a iya kare iyali da kamuwa da su.
1) Zazabin cizon sauro
Ana samun yawaitar yaduwar zazabin cizon sauro a damina saboda karuwar ruwa a magudanan ruwa da ramuka. Sauro na bukatar ruwa wajen kyankyanshe kwai hakan kuma ke kawo karuwar yaduwar cutar tunda sauro ne ke yada ta.
Domin kiyaye yaduwar cutar, masana suna shawartan mutane su tsaftace muhalinsu, zubar da shara da kuma yanke ciyayi da ke fitowa a harabar gida tare da tabbatar da cewa babu wani inda ruwa ke kwanciya barkatai. Wata hanuar kariyar kuma shine amfani da ragar saura a kofofi da taga ko gado.
2) Mura
Mura na iya kama mutane a kowanne yanayi amma tafi yawa da damina. Ita mura kayar cutar bacteria ne ke yada ta kuma kwayar cutar kan karu sosai da damina.
Hanyoyin da za'a iya kare kai sun hada da wanke hannu a kan kari da ruwa tare da sabulu da kuma amfani da tissue paper a maimakon hankici domin hankici na iya daukan kwayoyin cuta yayinda aka sanya ta a aljihu ko wani wurin daban.
Wata hanyar kariyar kuma shine sanya kaya masu dumu ga yara da hana su wasa da ruwa.
3) Ciwon idon Apollo (Conjunctivitis)
Conjunctivitis ciwon ido ne da akafi sani da Apollo wadda ke sanya idanu suyi jawur tare da kaikayi, kumburi da fitar da hawaye. Kwayar cutar bacteria ko virus ne ke janyo cutar kuma ana iya kamuwa idan an taba hawayen da ke fita daga idanun mai cutan.
Don kiyaye kamuwa da cutan, mutum ya guji amfani da hankicin wani kuma a rika wanke hanuwa a kan lokaci. Masana kuma sun shawarci mai cutar ya guji sanya gilashi domin kwayoyin cutar suna iya makalewa jikin gilashin.
4) Amai da gudawa (Cholera)
Cholera cuta ce da ke yaduwa ta hanyar ruwa kuma anfi kamuwa da ita lokacin damina. Ana iya kamuwa da cutan ta hanyar shan ruwa ko cin abincin mai dauke da kwayar cutar kuma yara kananan sunfi kamuwa da ita.
Ana iya kare kamuwa daga cutar ta hanyar yin rigakafi wanda ke amfani na tsawon watanni shida, sauran hanyoyin kariyar sun hada da amfani da ruwa mai tsafta, wanke hannu kafin cin abinci da bayan an gama, tsaftace ban daki da kuma zubar da bola nesa da gida.
5) Zazabin Typhoid
Typhoid cuta ce da ke yaduwa ta hanyar shan ruwa ko cin abinci da ya gurbata da bayan gidan wanda ke dauke da cutar, ita ma yara sunfi kamuwa da ita.
Alamominta sun hada da zazabi mai zafi, kasala, ciwon ciki, ciwon kai da rashin cin abinci. Ana iya gwajin gano cutar ta hanyar binciken bayan gidan mutum a asibiti. itama akwai rigafi na kamuwa da cutar.
Hanyoyin kare kai daga cutar sun hada da tsaftace muhalli, amfani da rwuan sha mai tsafta da wanke hannu a kan kari.
6) Hepatitis A
Wannan cuta ce da ke illa ga hantar dan adam wanda kwayar cutar virus ke janyowa.
Ana iya kamuwa da cutar da hanyar cin abinci da mai cutar ya taba, ko ruwan sha ko kuma taba jiki ko tufafin mai cutar musamman idan ya yi zufa.
Idan ba'ayi magani da wuri ba, cutar na yaduwa cikin sauri kuma tana iya yiwa al'umma da dama illa.
Cutar bata cika nuna alama ba musamman idan matasa ne suka kamu da ita, wasu daga cikin alamominta sun hada da tashin zuciya, amai, zazabi, ciwon ciki, rashin cin abinci da sauya launin idon mutum zuwa ruwan dorawa.
Akwai rigakafi na kare cutar, kazalika ana iya kiyaye kai ta hanyar amfani da ruwa mai tsaf, tsaftace muhalli da kuma yawaita wanke hannu
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng