Maganar ta tsaro ce: An shiga ganawar sirri tsakanin Buhari da Buratai (Hoto)
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanal janar Tukur Buratai, a yau, Alhamis, a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Da yake Magana da manema kabarai a fadar gwamnati jim kadan bayan fitowa daga ganawar sirri da shugaba Buhari, Buratai, ya ce alhakin sa ne yake yiwa shugaban kasa bayani a kan al’amuran sojin kasa lokaci zuwa lokaci.
Buratai ya bawa ‘yan Najeriya tabbacin cewar, hukumar sojin Najeriya zata cigaba da hada kai da ragowar hukumonin tsaro dake kasar nan domin tabbatar da tsaron lafiya, dukiyoyi, martaba da kimar Najeriya.
DUBA WANNAN: Kotun Najeriya ta yankewa wani mutum daurin shekaru 2,675, karanta laifin da ya aikata
Ya kara da cewa batun tura bataliyar sojoji zuwa Birnin Gwari dake jihar Kaduna, na bisa dokar aiyukan sojin Najeriya.
A bangaren yaki da ‘yan ta’addar Boko Haram, Buratai ya bayyana cewar tuni hukumar sojin Najeriya ta fara aikin gina wasu hanyoyi a dajin Sambisa domin tabbatar da nasarar kakkabe mayakan Boko Haram daga dajin tare da jaddada kudirin hukumar sojin na mayar da dajin Sambisa cibiyar shakatawa da yawon bude ido.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng