Ta faru ta kare: Buhari ya tona asirin dalilin da ya sanya aka yi masa juyin mulki a 1985

Ta faru ta kare: Buhari ya tona asirin dalilin da ya sanya aka yi masa juyin mulki a 1985

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sanya aka yi masa juyin mulki kuma aka tsare shi har na tsawon shekaru uku.

Muhammadu Buhari ya ce wadanda suka yi masa juyin mulki sun yankewa gwamnatinsa kwananta ne a dalilinsa na yaki da cin hanci da rashawa a 1985. Idan za’a tunawa jigo a gwamnatin Buhari ta waccan lokacin Ibrahim Babangida ne ya habbarar da mulkin nasa.

Bayan juyin Mulkin ne Ibrahim Babangida ya bayyana cewa saboda ya zama dole sakamakon dagulewar abubuwa da matsanancin rayuwar kunci da ‘yan Najeriya suke ciki ya sanya shi daukar matakin, amma sai dai shugaban Buhari a yau ya jaddada cewa, an yi masa juyin mulkin ne bisa kudirinsa na yaki da cin hanci da rashawa.

Ta faru ta kare: Buhari ya tona asirin dalilin da ya sanya aka yi masa juyin mulki a 1985
Buhari a mulkin soja

Amma a cewarsa ya riga da yasan tabbas mutukar zaka yaki cin hanci da rashawa to tabbas akwai wadanda ba za su so ba kuma za suyi duk mai yiwuwa wajen hanawa, sai dais hi hakan baya bashi tsoro.

“Fada a karon farko da Cin hanci da na fara, amma sai dai kash ‘yan Uba sunyi nasara a kai na har ma suka tubuke ni daga ofishi na.” ya shaida

Muhammadu Buhari ya cigaba da cewa, tun bayan da aka sake zabarsa a shekarar 2015 ya sake sabon salon a yakar cin hanci tare kuma da daukar matakai daban-daban da suka dace duk don a samu nasara a yakin da ake na dakile rashawar a tsakanin al’umma musamman masu rike da mukamin gwamnati.

KU KARANTA: Ba’a taba Kashi ba ma yayi wari balle an dakume shi: Anyi kira ga Magu da kada ya saurarawa Barayi

Bisa hakan ne ma ya sanya yanzu kowa ya yarda da cewa Barayin dukiyar talakawa basu da wata kwanciyar hankali domin ko ba jima ko ba dade tabbas za’a kama su.

Da yake mayar da martini bisa zargin yin son rai a bangaren wadanda hukumar ta EFCC take tuhuma, shugaba Buhari ya ce, “Ba shi da burin yin bi ta da kulli ko cuzgunawa kowa, amma idan kasan kana da kashi a gindi to sai kazo ka yiwa doka bayani.”

Daga karshe yayi kira ga Majalisar wakilai ne da karawa kudirin nasa na yaki da cin hancin ta hanyar yiwa tsofaffin dokokin ga kundin tsarin Mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng