Dalilin mu na kin goyawa Buhari baya - Kungiyar dattijan Arewa
Kungiyar dattijan Arewa (ACF) ta bayyana dalilin ta na kin bayyana goyon bayan ta ga takarar shugaba Buhari a zaben 219.
ACF ta ce 'yan Najeriya masu katin kada kuri'a ne kawai zasu raba gardamar waye zai zama shugaban kasar Najeriya a 219.
Sakataren kungiyar, Dakta Anthony Sani, ya soki shugaba Buhari bisa yin shiru da ya yi a kan kashe-kashen dake faruwa a wasu sassan Najeriya.
Da yake magana a kan dalilin da yasa ACF bata bayyana goyon bayan ta ga takarar Buhari, Sani ya ce, "kungiyar ACF uwa ce ga kungiyoyin dake magana da yawun mutanen arewa.
DUBA WANNAN: Jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC sun kauracewa taron zabukan jam'iyyar, An kashe mutum guda
Sannan ya cigaba da cewa, " ba hurumin ACF bane ta zabawa jama'a dan takarar da zasu zaba ba saboda ba kungiyar siyasa ba ce."
Kazalika ya ce bashi da tabbacin ko kungiyar ACF ta gamsu da kokarin shugaba Buhari a kan karagar mulki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng