Boko Haram za su mika wuya - Aisha Wakil

Boko Haram za su mika wuya - Aisha Wakil

Lauya mai kare hakin bil-adama da kuma yin sulhu, Hajiya Aisha Wakil wanda akafi sani da Mama Boko Haram tace a kwana-a-tashi mayakan kungiyar Boko Haram za su mika wuya kuma su koma gidanjensu.

A jawabin ta yi wajen taron neman taimako na gidauniyarta, a ranar Asabar a garin Maiduguri, Wakil ta ce 'yan Boko Haram din suna ta niyyar ajiye makamansu inda suka ce suna son su dawo gida wajen iyalensu.

Boko Haram za su miya wuya - Aisha Wakil
Boko Haram za su miya wuya - Aisha Wakil

KU KARANTA: Sojin saman Najeriya ta cika shekaru 54 da kafuwa, Kalli hotunan kayayakin yaki da suka mallaka

"Dukkan yara na da ke cikin daji za su fito kuma su mika wuya saboda a samu zaman lafiya," inji ta.

Mama Boko Haram tayi alkawarin cigaba da gwagwarmaya don ganin an samu zaman lafiya mai dorewa na jihohin da ake samun tashin hankula.

"Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen tin sulhu har sai na tabbatar an sako duk wadanda suke hannun 'yan Boko Haram."

A yayin da take tsokaci kan ayyukan gidauniyar ta mai suna 'Complete Care and Aid', ta ce an kafa gidauniyar ne saboda bayar da kulawa ga wadanda masifar ta'addancin ya shafa wanda suka hada da marayu da wandanda suka rasa muhallinsu.

Wakil ta ce gidauniyar za ta bayar da gudunmawa a bangarorin ilimi, kiwon lafiya da taimakawa wadanda rikicin ya shafa ta hanyar shawarwari da tallafi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel