An sake bude makarantar sakandire na 'yan mata da ke Dapchi

An sake bude makarantar sakandire na 'yan mata da ke Dapchi

- Gwamnatin jihar Yobe ta sake bude makarantar sakandire na yan mata da ke garin Dapchi

- Rufe makarantar ya biyo bayan sace yan matan 113 da mayakan Boko Haram sukayi a kwanakin baya

- Duk da cewa gwamnatin da ceto yan matan, galibin iyayen yara suna dar-dar kan batun sake mayar da yaransu makarantar

Rahotanni da muka samu daga wata majiya sun bayyana cewa gwamnatin jihar Yobe ta bayar da umurnin sake bude makarantar sakandire na yan mata da ke Dapchi, wannan yana zuwa ne bayan gwamnati ta ceto 'yan matan da ake sace kwanakin baya daga hannun yan Boko Haram.

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, gwamnatin ta bayar da tabbacin samar da ingantaciyar kariya ga daliban da kuma daukan matakai na ganin harin da ake kai makarantar bai sake afkuwa ba.

An sake bude makarantan sakandire na 'yan mata da ke Dapchi
An sake bude makarantan sakandire na 'yan mata da ke Dapchi

DUBA WANNAN: An sallami Farfesa da wani malami daga Jami'ar ATBU ta Bauchi

Gwamnatin tana kira da iyayen daliban makarantar sakadaren da su kokarta su sake turu yaransu makarantar don su cigaba da karatunsu ba tare da wani bata lokaci ba.

Sai dai a yayin da manema labarai suka tuntubi shugaban kungiyar iyayen dalibai na makarantar ko sun san da sanarwan dawo da yaransu, Malam Bashir Manzo yace bai samu sanarwan bude makarantar a hukumance ba amma ya kira sakataren ma'aikatar ilimi kuma ya tabbatar masa.

Da aka sake tamabayarsa ra'ayinsa a kan bude makarantar da gwamnatin jihar ta sake yi, Manzo ya kada baki ya ce "gaskiya zaiyi wahala mafi yawan iyayen su amince su mayar da yaransu wannan makarantan."

Ya kuma kara da cewa akwai bukatar gwamnati tayi wasu muhimman gyare-gyare da daukain matakan tsaro na musamman kafin sake bude makarantan ba wai kwatsam a sake bada umurnin iyaye su tura yaransu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel