Gwamnatin tarayya ta bayyana inda dumbin kudi da kadarorin da aka kwato suke

Gwamnatin tarayya ta bayyana inda dumbin kudi da kadarorin da aka kwato suke

Mutane sun fara shakkun alkaluman kudaden da aka kwato ne, tun daga abinda mai rikon mukamin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (EFCC) Ibrahim Magu ya ce: sun yi nasarar kwato Naira Bilyan 739, da kuma abinda ministan kudi Kemi Adeosun ita ma ta fada cewa: su abinda suka gani a asusun gwamnatin tarayya wanda aka kwato, bai wuce Naira bilyan 91.4 ba, tun shekarar 2015 zuwa yanzu.

Babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa Malama Juliet Ibekaku ta ce, kafatanin dukiyar da aka kwato, an juya su zuwa kadara ta musamman a babban bankin kasar nan CBN, amadadin su kuma sai a turo kudi zuwa asusun tarayya, da su ne kuma aka rinka amfani da su wajen kasafin shekara-shekara tun a 2017.

Ibekaku-Nwagwu, wadda ita ce shugaba mai sa-ido na Nigeria’s Open Government Partnership (OGP), cewa ta yi:

Gwamnatin tarayya ta bayyana inda dumbin kudi da kadarorin da aka kwato suke
Shugaba da jami'an hukumar EFCC

"Kamar yadda da wasun ku suka sani, gwamnati ta yi kokari matuka na dawo da dukiyar da aka sace. Hatta kudaden mu dake Switzerland wanda Abacha ya sace, an bayyana yadda za'a kashe su da zarar sun iso hannun gwamnati, kamar yadda wasu kasashen suke yi."

DUBA WANNAN: Kalli hotunan rayuwar mutane a garin Offa dake jihar Kwara bayan harin 'yan fashi na ranar 5 ga watan Afrilu

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, tun farkon fara kwato kudaden ne, shugaba Muhammadu Buhari a kashin kansa, ya ga dacewar fitar da wasu ka'idojin yadda za'a yi da kudaden. Don haka ya umarci da a rinka ajiye kudaden a matsayin kadara ta musamman a babban banki kasa.

"Daga can ne, za'a juya su zuwa asusun tarayya don a rinka cike gibin kasafi da su. Za mu iya fahimtar an yi haka tun a kasafin shekarar 2017." A cewarta

DUBA WANNAN: Gwamna ya zubar da hawaye bayan rattaba hannu a kan kasafin kudi, karanta dalilinsa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel