An kashe mutane 24 a wata sabuwar harin da makiyaya suka kai Binuwai - Majalisa

An kashe mutane 24 a wata sabuwar harin da makiyaya suka kai Binuwai - Majalisa

- Mambobin Majalisar wakilai sun bayyana cewa makiyaya sun sake kai hari a jihar ta Binuwai

- Mambobin sun bukaci hukumar Soji da ta gaggauta kai dauki a kauyukan da ake yawan kaiwa hari

- Mambobin sun bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya makiyaya a matsayi ‘yan ta’adda

A ranar Alhamis ne mambobin majalissar wakilai suka janyo hankalin majalisar kan sabbin hare-haren da makiyaya suka sake kaiwa a wasu garuruwan da ke jihar ta Binuwai.

Mambobin sun bukaci hukumar Soji da ta gaggauta kai dauki a kauyukan na jihar ta Binuwai wadanda ake yawan kaiwa hari, wanda ya sabawa aikin da Sojin keyi na Operation Cat Race.

An kashe mutane 24 a wata sabuwar harin da makiyaya suka kai Binuwai - Majalisa
An kashe mutane 24 a wata sabuwar harin da makiyaya suka kai Binuwai - Majalisa

Mambobin sun bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya makiyaya a matsayi "yan ta’adda”. Sukace misali ranar 2 da 4 ga watan Afirilu, mambobin sunce a kalla mutane 24 aka kashe sannan dayawa sun bace.

DUBA WANNAN: Shugabanin addinin kiritsa sunki amincewa da tazarcen Buhari

Mambobi hudu wadanda sukayi magana akan rikicin Binuwai sun hada da Dickson Takighir; Mark Terseer-Gbillah; Samuel Udende; da John Dyegh, wadanda sukace anyi kisan ba tare da jami’an tsaro sun kawo wani dauki ba.

Mambobin sunce an nuna rashin adalci akan daukin Operation Cat Race saboda hukumar Sojin ta tsayar dashi a jihar ta Binuwai, amma ta kara masa wa’adi a wasu jihohin wanda ya hada da jihar Taraba.

Takighir yace kisan da akayi na karshe anyi shi ne a Ikyon da Agasha a ranar 3 da 4 ga watan Afirilu, a Semaka, Asom, Babanruwa kuma anyishi shima a ranar 3 ga watan Afirilu, sai Udei da Umenger a ranar 2 ga watan Afirilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164