Kiwon lafiya: Amfani da na’urar dumama abinci yana jawo cuta iri-iri
Masana sun gano cewa amfani da na’urar dumama abinci da ake yin a zamani yana jawo cututtuka ga mutum. Irin wannan na’ura ta microwave tana dauke sinadaran kirki da ke cikin abinci sannan kuma a sa wasu sinadaran masu illa a abinci.
Da dama dai ba su san illar da irin wadannan na’urori na zamani su ke yi ba amma yanzu bincike ya nuna cewa gara mutum ya dafa abincin sa ya ci a nan-take a kan ya dafa sai daga baya yayi amfani da na’urar microwave ya dumama saboda karancin sukuni.
Daga cikin cututtukan da wannan na’ura ta dumame ke jawowa akwai:
KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya ba 'Yan Najeriya muhimiyyar shawara
1. Matsalar haihuwa
2. Kashe kwayoyin garkuwan jiki
3. Rage yawan Hemoglobin a jikun mutum
4. Rage wasu sinadarai a cikin jini
5. Kashe kwayoyin ran ‘Dan Adam
6. Hana barci
7. Kashe kwakwalwa
8. Nauyi
9. Karawa mutum Cholestrol
10. Ciwon zuciya
11. Kasala da
12. Cutar zuciya
Asali ma dai ba a so mutum ya tsaya kusa da irin wadannan na’ura idan su na aiki domin kuwa su na amfani da wani irin zafi da zai iya jawowa mutum nakasa ba ma abincin sa ba kurum.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng