Ba A Taba Shugaban Nijeriyar Da Ya Kama Kafar Buhari a Yaki Da Cin Hanci Ba - Adeniran
Debo Adeniran, shine shugaban wata cibiya dake rajin yaki da cin hanci da kuma shugabanci na gari a Nigeria wato CACOL a takaice.
A wata hira da yan jarida suka yi da shi, Adeniran ya bayyana shugaba Buhari a matsayin gwarzon da ya sami nasarori da dama musamman a bagare yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin sa fiye da duk wani shugaba da Nigeria ta taba yi.
Da aka tambaye shi kan nasarorin Buhari a bangaren yaki da cin hanci da rashawa?
Adeniran yace: "Zuwa yanzu dai kam sai sam barka. Babu wanda ya tabuka abin a yaba a baya a wannan bangaren a baya. An yi kwamacala da yawa a baya. APC bata kai shekara guda da kafuwa ba sa'adda ta sami mulki. Su kansu ba su fahimci kansu sosai ba. Baza ka hada su da jama'iyyar da ta share shekara 16 ba. Yan APC ba su taba aiki tare ba kafin samun mulki ba. Buhari bai taba aiki da su ba. Wasun su kan iya yaudarar sa ya nada su mukami, kuma sai a kwashe shekara ko shekaru kafin a gano mabarnata ne."
DUBA WANNAN: Dalilina na watsi da sunan sarautar Yoruba da rungumar na Hausa
"Ina fada muku yaki da cin hanci ba karamin abu ba ne. Shi yasa kake jin sabanin ra'ayi a bangaren gwamnati, yan majalisu da bangaren shari'a. Da yawa cikin yan majalisar dattijai na da kashi a gindinsu. Amma Buhari yayi hikima a kirkiro da asusun bai-daya (TSA) da kuma tsarin BVN. Buhari kadai ba zai iya sa ido kan kowa ba, amma in kana da gwarzo kamar Magu a matsayin shugaban EFCC, ya nuna da gaske kake wajan fada da cin hanci a kasar nan" Inji Adeniran
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng