Shugaban kasar Botswana ya sauka daga mulki
A wannan makon, Shugaba Ian Khama na kasar Botswana ya kammala ziyarar bankwana da al'ummar kasar kafin ya sauka daga mulki a ranar Asabar inda zai mika mulkin ga mataimakin sa don rikon kwarya kafin gudanar da wata zaben.
Khama ya ziyarci dukkan yankuna 57 da ke kasar tun a watan Disamba da ta shude inda ya yi bankwana da al'umma fiye da miliyan 2.2 bayan ya shafe shekariu 10 kan karagar mulki kamar yadda kundin tsarin kasar ya bayar da dama kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Mataimakin shugaban kasa Mokgweetsi Masisi ne zai karba ragamar mulkin kasar har na tsawon watanni 18 kafin a gudanar da zabe a kasar.
KU KARANTA: Faduwar jarabawar WAEC: Majalisa ta bukaci Ministan Ilimi ya bayyana a gaban ta
A tsawon mulkin da Khama ya yi a kasar, an samu cigaba sosai a fannin tattalin arziki musamman fannin fitar da fitar da hajja zuwa kasuwanin kasasen waje wanda suka hada da nama da kuma zinari.
Al'ummar kasar sun jin dadin mulkin sa musamman yadda aka san shi da fadin gaskiya ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba, misalin hakan shine yadda ya rika cacakar shugaban kasar Amurka Donald Trump da tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe.
Ya kammala ziyarar bankwanar ta sa ne a kauyen su mai suna Serowe wanda ke gabashin kasar inda dumbin al'umma suka tarbe shi da wakoki, kyaututuka har ma da masu rokon sa ya cigaba da mulkin.
Sai dai ya fadawa al'ummar cewa "Ni soja ne, bani da ra'ayin shiga siyasa. Ina da wasu tsarin nawa wanda basu shafi siyasa ba," ya kara da cewa sai da tsohon shugaban kasa Festus Mogae ya roke shi kafin ya karbi mulkin a shekarar 2008.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng