Jami'an tsaro sun kama mai daukar nauyin masu sace mutane a jihar Kogi
- Jami'an DSS sunyi nasarar cafke wanda ake zargi yana tallafawa kungiyar garkuwa da mutane na Basalube da kudi da makamai
- An kama Lawal Muhammed tare da wasu yan kungiyar guda biyu a wata samame da aka a ranar 23 ga watan Maris
- Kungiyar da ta shawara wajen satar al'umma a jihohin Kebbi, Kaduna, Edo, Delta, Ribas, Zamfara da babban birnin tarayya, Abuja
A yau Talata ne hukumar Yan Sandan farin kaya (DSS) ta bayar da sanarwan kama wani mutum, Lawal Mohammed da ake zargin yana tallafawa gagararun yan kungiyar masu garkuwa da mutane na Basalube a jihar Kogi.
Sanarwan da ta fito daga bakin mai magana da yawun hukumar a Abuja, Mr. Tony Puiyo ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 23 ga watan Maris a garin Japama na karamar hukumar Obajana da ke jihar Kogi.
KU KARANTA: Hukumar kwastam ta kama buhunan shinkafa 589 a cikin motar dakon man fetur
Opuiyo ya ce jami'an DSS da kuma Sojoji ne suka kama wanda ake zargin ne tare da yan kungiyar Basalube guda biyu, Mohammed Tukur da Abubakar Ibrahim a wani samame da suka kai.
Ya ce an gano cewa Tukur ne mai yiwa kungiyar sharen fage da bibiyar musu titi tsakanin jihohin Ribas, Edo, Delta, Kaduna, Zamfara, Kebbi da kuma babban birnin tarayya Abuja kafin su fita satar mutane.
Opuiyo ya ce jami'an hukumar ta DSS sun kwace wayoyin salula guda uku tare da kwallaben kayan maye guda 25.
Hakazalika, DSS din ta ce ta damke wasu mutane biyar da ake zargin yan kungiyar satar mutanen ce ta Basulube a karamar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta.
Wadanda aka kama sun hada da Ali Abubakar, Abdulkareem Idrisa, bashir Tsoho, Sanusi Abubakar, Nuhu Muhammad da kuma Abubakar Abdulhameed. An kama su yayin da suke kokarin satar mutane a Obajana.
Opuiyo ya ce hukumar ta DSS ta dau alwashin ganin bayan kungiyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng