Gwamnati za ta karbi tubar 'yan Boko Haram da suka mika wuya - Buhari
- Shugaba Buhari ya karbi ‘yan matan makarantar Dapchi da aka saki kuma ya bayyana cewa zai karbi mika wuyan Boko Haram
- Shugaban kasar ya kara da cewa gwamnatinsa a shirye take da ta bawa wadanda suka mika wuya kula ta musamman
- Yace gwamnati na iyaka gwargwadon kokarinta don ganin cewa an saki kowane dan kasa dake hannun ‘yan ta’adda
Shugaba Muhammadu Buhari a jiya, a ofishinsa, a birnin tarayya, ya karbi ‘yan matan makarantar Dapchi da aka saki kuma ya bayyana cewa zai karbi tubar 'yan kungiyar Boko Haram da suka ajiye makamai kuma suka mika wuya.
Shugaban kasar ya kara da cewa gwamnatinsa a shirye take da ta bawa wadanda suka mika wuya kula ta musamman don ci gaba da rayuwa a cikin wannan al’umma tamu mai girma.
Yace, “gwamnati na iyaka gwargwadon kokarinta don ganin cewa an saki kowane dan kasa dake hannun ‘yan ta’adda”.
KU KARANTA: Matsayar da muka cinma da kungiyar Boko Haram kafin sakin 'yan matan Dapchi - Lawal Daura
Shugaban kasar ya gargadi shuwagabannin tsaro akan cewa idan aka samu wata baraka ko yaya ta ke daga bangarensu, za'a hukunta su. Yace, ya rataya wa dukan jami’an tsaro nauyin kiyaye kara aukuwar satar ‘yan makaranta a duk fadin kasar nan.
A kokarin da gwamnatinsa ke yi na yaki da ta’addanci, Buhari bukaci dukan ‘yan Najeriya da su taimaka wurin gudanar da wannan aiki. Shugaban kasar yace, kasar ta wahala sosai, don haka yana so kowa ya rungumi zaman lafiya saboda cigaban kasar.
A lokacin da ta ke jawabi a mamadin ‘yan uwanta, Fatima Bashir mai shekaru 14, ‘yar aji uku, tayi godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya ceto rayuwarsu daga hannun ‘yan ta’adda, ya kuma dawo dasu gidajen su lafiya
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng