'Yan bindiga sun kai hari sansani soji a Kaduna, sojoji 11 sun rasa rayyukansu
- Wasu yan bindiga sun kai farmaki a sansanin sojojin Najeriya da ke garin Maganga a jihar Kaduna
- A kalla sojoji 11 ne suka rasa rayyukansu sakamakon artabun da akayi da yan bindigar, wasu kuma sun jikkata
- Hukumar Sojin da Gwamnatin jihar Kaduna sun ce za suyi bayyani kan lamarin bayan sun gama kamalla bayanai
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji guda 11 ne suka rasa rayyukansu a wani hari da wasu yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba suka kai a sansanin sojoji da kegarin Kamfanin Doka a hanyar Funtua da ke karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.
Jaridar Premium Times ta tabbatar da cewa harin ya faru a daren jiya Talata.
Hakazalika, wani tsohon shugaban karamar hukuma da ya nemi a sakaya sunnan sa saboda bashi da izinin tsokaci kan lamarin ya tabbatar da faruwar harin.
KU KARANTA: Nayi murna da farin ciki sosai game da sakin 'yan matan Dapchi - Mama Boko Haram
Ya kara da cewa bayan wandanda suka rasu, wasu sojojin uku da kuma wasu yan banga sun sami raunnuka.
"Yan bindigan sun kai hari ne a sansanin sojojin da ke Kamfanin Doka a hanyar Funtua. Sojoji 11 sun rasa rayyukansu kuma wasu 3 sun jikata.
"Yan bindigan har ila yau sun kai farmaki ga yan banga a Maganga, wani gari da ke kilomita 44 daga Birnin Gwari a safiyar Laraba a yayin da suka je taimakawa sojojin. Guda tara sun sami raunuka, an garzaya da su asibiti a halin yanzu," inji shi.
Ya yi bayannin cewa yan bindigan sun iso ne a kan babur misalin karfe 10,05 na dare a daren Talata inda sukayi ta artabu da sojojin.
Yayin da aka tuntubi jam'in hulda da jama'a na One Mechanised Division, Mohammed Dole, ya ce: "A halin yanzu muna cikin daji don tattara bayanai kan abin da ya faru. Zamu fitar da sanarwa bayan mun kammala bincike, a kara hakuri."
Hakazalika, mai magana da yawun gwamnan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce gwamnati za tayi tsokaci kan lamarin indan sun sami bayannai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng