Ronaldo ya shiga sarkakiya, akwai yiwuwar ba zai samu zuwa gasar cin kofin Duniya ba

Ronaldo ya shiga sarkakiya, akwai yiwuwar ba zai samu zuwa gasar cin kofin Duniya ba

  • Hukumar kwallon kafa ta hada Portugal da kasar Italiya a rukuni daya na zuwa gasar kofin Duniya
  • Kasashen Duniya za su fafata a kasar Qatar ba tare da zakarun na Turai na shekarar 2016 da 2021 ba
  • Haka zalika daya zai je gasar Duniya tsakanin Wales da Scotland da kuma Sweden da Macedonia

A ranar Juma’a, 26 ga watan Nuwamba, 2021, aka shirya wasan sharar fage zuwa kofin Duniya ga kasashen da ba su samu shiga gasar kai-tsaye ba.

FIFA ta shirya duron gasar kofin na kasashen Duniya, inda aka hada Italiya da Portugal a rukuni guda, hakan ya na nufin daya kadai ne zai yi nasara.

Marca tace kasar Italiya za ta fara buga wasa ne da North Macedonia, yayin da Portugal za ta gwabza da Turkiyya a wasannin sharar fagen a 2022.

Kara karanta wannan

Beluga, Onavo da wasu kamfanoni 3 da Zuckerberg, mai kamfanin Facebook ya saye

A gasar da za a buga a Qatar a shekarar badi, tsakanin zakarun nahiyar Turai masu-ci, kasar Italiya da zakarun na shekarar 2016, za ayi babu wani.

Jaridar ta Marca tace da yammacin Juma’ar nan aka bada sanarwar duron wasannin sharar fagen.

Ronaldo
Cristiano Ronaldo Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ya aka yi haka?

Portugal ta samu kanta a cikin halin ha’ula’i ne bayan ‘yan wasan Fernando Santos sun gagara doke Serbia a zagayen wasan karshe da suka buga.

Sai Cristiano Ronaldo da ‘yan wasan kasar Portugal sun yi da gaske idan su na son zuwa Qatar, domin ‘yan wasan kasar Italiya ba kanwar lasa ba ne.

Su kuma kasar Italiya sun yi canjaras a wasan da suka buga da kasar Ireland. Hakan ya ba Switzerland damar zuwa gasar Duniyan kai-tsaye.

Kara karanta wannan

Minista tayi karin-haske kan yadda za a biya talakawa N5000 bayan cire tallafin mai a 2022

Sauran wasannin da za a a buga

A daidai wannan lokaci kuma an ji cewa shi ma ‘dan wasa Zlatan Ibrahimovic yana cikin irin wannan yanayi, an hada Sweeden da Czech Republic.

Rukuni na gaba shi ne tsakanin Scotland da Ukraine, wanda ya yi nasara a cikinsu zai gwabza da wanda ya lashe wasansa tsakanin Wales ko Austriya.

Benzema bai da gaskiya?

A makon nan ne ku ka ji cewa Alkali ya kama ɗan wasan gaban kungiyar Real Madrid da ke kasar Sifen watau Karim Benzema da laifin cin amana.

Rahotanni tace kotu ta samu ɗan kwallon kafan ne da laifin da ake tuhumarsa da shi na cin amanar wani tsohon abokin wasansa, Mathieu Valbuena.

Asali: Legit.ng

Online view pixel