Minista tayi karin-haske kan yadda za a biya talakawa N5000 bayan cire tallafin mai a 2022

Minista tayi karin-haske kan yadda za a biya talakawa N5000 bayan cire tallafin mai a 2022

  • Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattali ta yi karin bayani a kan tsarin biyan talakawa N5, 000
  • Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta ba marasa karfi kudi idan an janye tallafin man fetur a 2022
  • Zainab Ahmed tace gwamnatin tarayya ba za ta wuce shekara guda tana bada wadannan kudi ba

Abuja - Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta yi karin haske a game da shirin raba N5, 000 ga marasa karfi a shekara mai zuwa.

Gwamnatin Muhammadu Buhari na kokarin janye tallafin man fetur a 2022, don haka za a rabawa talakawa N5, 000 domin su rage rade-radin tsadar man fetur.

This Day ta rahoto Zainab Ahmed ta na cewa za a biya wannan alawus ne na tsawon shekara daya rak domin gwamnati ba za ta iya yin abin da ya wuce hakan ba.

Kara karanta wannan

Bankin Afrika zai ba Gwamna Ganduje Dala miliyan 110 domin ayi ayyuka a kauyukan Kano

Da take magana da ‘yan jarida bayan taron majalisar FEC da aka yi a fadar shugaban kasa a birnin Abuja, Ahmed tace tallafin ba zai zarce watanni shida zuwa 12 ba.

Yaushe za a daina biyan kudin?

“Kuma har yanzu kwamitin ya na kan aiki. Saboda haka nan da Litinin za mu sani yadda za ayi, nawa za a kashe, yadda za a biyowa lamarin a kowace jiha.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari
Shugaban kasar Najeriya Hoto: @GarShehu
Asali: Facebook

“Zuwa yaushe za a daina bada wannan tallafi? To, mu ce watanni shida zuwa 12.” – Ahmed.

Jihohi za su iya biyan abin da ya dara N5, 000

Ministar kudin tace wasu jihohi na iya bada tallafin da ya zarce N5, 000, amma gwamnatinn tarayya ta kai bango, ba za ta iya yin abin da ya wuce wannan ba.

“Gwamnati na kokarin bada gudumuwa, mun so a ce za mu iya yin abin da ya wuce haka. Amma a takure mu ke a game da adadin abin da za mu iya biya.”

Kara karanta wannan

Wahalhalu 5 da 'yan Najeriya za su shiga idan man fetur ya koma N340, Shehu Sani

“Amma babu abin da zai hana jihohi bada kari a kan wannan N5, 000 da za a biya daga tarayya.”

Jaridar tace baya ga batun tallafin man fetur, Ministar tayi bayani a kan nasarar da tattalin arziki ya samu a tsakiyar shekarar nan kamar yadda alkaluma suka nuna.

Ba a ware kudin da za a rabawa talakawa ba?

A ranar Larabar nan ne majalisar dattawan kasar nan tace ba ta gida inda aka yi kasafin kudin da ake cewa za a rabawa marasa karfi idan litar fetur ya dawo N340 ba.

Sanata Adeola Solomon yace gwamnati ba ta isa ta batar da tiriliyoyi haka kurum ba. Sanatan yace dole sai majalisa ta ga yadda za a zakulo mutanen da za a ba kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng