Abin ya yi yawa: Manchester United ta fara tunanin sallamar Koci Ole Gunnar Solskjaer

Abin ya yi yawa: Manchester United ta fara tunanin sallamar Koci Ole Gunnar Solskjaer

  • Ana rade-radin Manchester United ta fara lissafin sallamar Ole Gunnar Solskjaer
  • An taso kocin a gaba ne bayan bulaliyar da Liverpool ta yi wa Manchester a gida
  • Tun da Ole Gunnar Solskjaer ya karbi ragamar kungiyar, bai taba cin wani kofi ba

England - An taso babban mai horas da ‘yan wasan Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer a gaba a sakamakon shan kashin da ya yi a hannun Liverpool.

Goal.com tace wasu daga cikin ‘yan kwallon kungiyar Manchester United sun karaya da kocin da masu horas da su, suna ganin ba za su iya kai su ga nasara ba.

Ko da cewa ‘yan wasa da-dama suna kaunar Ole Gunnar Solskjaer, akwai taurarin da suke ganin kocin ba zai iya ceto kungiyar daga halin da ta fada ciki ba.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

‘Yan kwallon kulob din sun yi la’asar tun da Leicester City ta doke su a filin wasa na King Power Stadium. Daga nan kuma suka sha da kyar a hannun Atlanta.

Abin ya yi yawa: Manchester United ta fara tunanin sallamar Koci Ole Gunnar Solskjaer
Bruno, Ole Gunnar Solskjaer da Ronaldo Hoto: www.goal.com
Asali: UGC

Halin da ake ciki a Manchester United

Solskjaer ya jefa Manchester United a matsayi na bakwai a teburin firimiya. Akwai maki takwas tsakanin kungiyar da wadanda suke kan samun teburin BPL.

A cikin wasanni hudu da kungiyar Manchester United na karshe, maki daya rak ta iya samu a Ingila.

Wasu suna ganin karawar Jurgen Klopp da Manchester United ta sake fito da gazawar Solskjaer. Har ‘yan wasan Manchester United sun yarda sun yi abin kunya.

Mohammed Salah ya jefa kwallaye uku a wasan da aka dirkawa Man Utd kwallaye biyar. Salah ne ‘dan wasan Liverpool da ya fara cin kwallo uku a Old Trafford.

Kara karanta wannan

Jerin wasanni 6 da aka zazzaga wa Manchester United kwallaye a Tarihin Premier

The Manchester Evening News tace Man United ta fara tunanin raba jiha da Ole Gunnar Solskjaer kafin haduwarsu da kungiyar Tottenham a karshen makon nan.

Tun da Solskjaer ya maye gurbin Jose Mourinho a Old Trafford, har yanzu bai ci wani kofi ba. Kwanan nan zai buga da Tottenham, Chelsea da Manchester City.

An ci Jose Mourinho 6 a Turai

A ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021, kungiyar Bodo/Glimt ta doke AS Roma ta kasar Italiya a gasar Europa Conference League na nahiyar Turai.

Jaridar Metro tace Jose Mourinho ya yarda ya dauki nauyin wannan kashin da kungiyar da yake horaswa ta sha a matsayinsa na kocin ‘yan wasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel