Mourinho ya sha mummunan kashi a hannun karamin kulob, an dirka masa kwallaye 6

Mourinho ya sha mummunan kashi a hannun karamin kulob, an dirka masa kwallaye 6

  • AS Roma ta sha kashi a hannun kungiyar Bodo/Glimt a filin Aspmyra Stadion
  • Wannan ne karon farko da aka ci Jose Mourinho kwallaye shida a wasa guda
  • Mourinho ya sake shan kunya a Turai bayan karawarsa da D/Zagreb a 2020/21

Norway - A ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021, kungiyar Bodo/Glimt ta doke AS Roma ta kasar Italiya a gasar Europa Conference League.

Jaridar Metro tace Jose Mourinho ya yarda ya dauki nauyin wannan kashi da kungiyar da yake horaswa ta sha a matsayinsa na kocin ‘yan wasan.

Tsohon kocin Man Utd, Jose Mourinho ya koka da cewa lafiyayyun ‘yan kwallo 13 kadai yake da shi.

Kafin jiyan, AS Roma ba ta rasa maki a gasar karamin kofin na nahiyar Turai ba. Wasan da aka buga a filin Aspmyra Stadion ya rusa wannan tarihi.

Read also

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Kafin a je ko ina, Erik Botheim da Patrick Berg suka jefa kwallaye biyu a ragar kungiyar ta Roma. Botheim ya sake cin wata kwallo kafin a cika sa’a.

Mourinho
Mourinho a wasan AS Roma v Bodo/Glimt Hoto: metro.co.uk
Source: UGC

Shi ma Ola Solbakken ya ci kwallaye biyu tsakanin minti na 70 zuwa na 80. ‘Dan wasan gaban kasar Norwegia, Amahl Pellegrino ya sa daya a raga.

Carles Perez ya sa kwallo daya a ragar Bodoe/Glimt, amma hakan bai hana kungiyar zama saman AS Roma da CSKA Sofia da Zorya a rukuninsu na 'C' ba.

Wannan wasa ya tuna wa magoya baya yadda Jose Mourinho ya yi asarar kwallaye uku a zagaye na biyu na wasan Tottenham da Dinamo Zagreb a bara.

Mourinho ya ajiye bakin tarihi

Kusan wannan ne karon farko da aka dirka wa kungiyar Mourinho kwallaye har shida a raga.

Read also

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Barcelona ta taba cin Real Madrid 5-0 a 2010, bayan shekaru uku Dormund ta yi galaba a kansa da ci 4-1. Chelsea ta taba cin Mourinho 4 – 0 a Manchester.

Tseren Ballon D'or

Ronaldo Delima ya yi magana game da takarar kyautar Ballon d'Or na wannan shekara. Tsohon ‘dan wasan na Brazil ya fadi wanda ya dace ya lashe kyautar.

Ronaldo mai shekara 45 yace Karim Benzema ne ‘dan wasan da ya fi dace wa da Ballon d 'or, har yana ganin yana gaba da Lionel Messi da su Cristiano Ronaldo.

Source: Legit

Online view pixel