Siyasar Najeriya
Matasan Arewa, sun ce ya kamata Obasanjo ya kira taron gaggawa na iyayen kasa, domin a samawa Najeriya mafita daga matsalolin da take fuskanta a yanzu nan.
Tsohon shugaban jam'iyya mai mulki APC, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa Allah zai taimaki yan Najeriya a shekarar 2023 dake tafe, babu abin tsoro.
Bishop Mike Okonkwo na The Redeemed Evangelical Mission (TREM) yayi magana akan dalilin da yasa baya son dan kudu maso gabas ya zama shugaban Najeriya na gaba.
Sanata mai wakiltar yankin Nasarawa ta Yamma, Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyyar PDP ba za ta taba zama barazana ga APC mai mulki ba a babban zaben kasar na 2023.
Yayin da rikici ya ki ci yaki cinye a cikin babbar jam'iyyar hamayya PDP, wata kotu a jihar Kebbi, ta soke hukuncin dakatar da Uche Secondus, ta sake maida shi.
Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya yi zargin cewa wasu daga cikin 'yan siyasar nan ne suka jefa kasar a halin da take ciki saboda son zuciya.
Babban malamin coci, Fasto Tunde Bakare, yace ba wani abun damuwa bane idan arewa sun fitar da wanda zai gaji shugaba Buhari a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Yayin da rikicin cikin gida ya kara barkewa a babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, jam'iyyar ta sanar da dage taron kwamitin zartarwa da aka shirya gudanarwa yau.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ba da tabbacin cewa za a karfafa babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party don karbe mulki a 2023.
Siyasar Najeriya
Samu kari