2023: PDP bata da tasiri kuma, ba za ta iya yi wa APC barazana ba - Sanata Adamu

2023: PDP bata da tasiri kuma, ba za ta iya yi wa APC barazana ba - Sanata Adamu

  • Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da wani tasiri a siyasar kasar a yanzu
  • Adamu ya ce jam'iyyar adawar ba za ta iya zama barazana ga APC mai mulki ba a babban zaben 2023
  • Jigon na APC ya kuma jadadda cewa jam'iyyar adawar ce ta jefa kasar a halin koma baya sakamakon mulkinta na shekaru 16

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma Sanata mai wakiltar yankin Nasarawa ta Yamma, Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fito ne saboda gazawar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi a kan mulki.

A cikin wata hira da jaridar Daily Trust, Adamu ya ce PDP wacce a yanzu ita ce babbar jam’iyyar adawa a kasar nan ta rasa tasirinta a siyasa kuma ba za ta zama barazana ga jam’iyyar APC mai mulki a babban zaben 2023 ba.

Kara karanta wannan

Ka Ji Kunya: Sadaukin Shinkafi ya soki Mataimakin Gwamnan Zamfara kan ƙin sauya sheƙa zuwa APC

2023: PDP bata da tasiri kuma, ba za ta iya yi wa APC barazana ba - Sanata Adamu
Sanata Adamu ya ce PDP ba za ta iya yiwa APC barazana ba a babban zabe mai zuwa Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Ya ce:

“Su (PDP) suna rasa karfinsu. Sun rasa gwamnoni uku masu zaman kansu zuwa APC kuma akwai sauran masu zuwa. Yanzu haka jam’iyyar ta rabu biyu kuma wasu daga cikin jiga -jigan jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC. Don haka, babu wata jam'iyyar da ta rage a matsayin PDP da za ta yi wa APC barazana.
“Lallai ya yi muni ƙwarai saboda muna son hamayya mai ƙarfi da za ta baje kwanji da jam’iyya mai mulki. Amma babu adawa a Najeriya a yau. Suna kasawa. Ba sa ba da kyakkyawan bayani game da damar da suka samu.
“Tushen gazawar kasar nan tun zuwan dimokradiyya shi ne gazawar PDP da ta yi mulki tsawon shekaru 16. Rashin nasarar PDP bayan shekaru 16 a kan mulki ne ya kawo APC. Kuma suna so su zarge mu saboda gazawarsu.

Kara karanta wannan

PDP: Gwamnatin Buhari na amfani da EFCC wajen cin zalin 'yan adawarta na PDP

“Duk yadda mutane suka kai ga sukar APC, akwai iyakar abin da za su iya yi kuma ba da jimawa ba, mutane za su gani ta hanyar makirci da karya da ake yadawa kan APC mai mulki. Muna kan hanya kuma za mu ci gaba da kasancewa kan hanya da yardar Allah.”

Dangane da burinsa na son zama shugaban APC na kasa, Adamu ya ce ba zai hana kansa bacci ba kan batun.

Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

A wani labarin, tsohuwar Ministar sufurin jirgin sama, kuma Sanata mai wakiltar Anambra a majalisar dattawa, Stellah Oduah, ta fita daga jam'iyyar People Democratic Party (PDP).

Bayan fitar ta, Stella Oduah ta sanar da manema labarai komawarta jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng