Rikicin Cikin Gida: Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matakin da Ta Dauka Bayan Kotu ta Dakatar da Shugabanta, Secondus
- Jam'iyyar PDP ta sanar da ɗage taron kwamitin zartartarwa (NWC) da aka tsara za'a yi yau Talata
- Mataimakin shugaban PDP (Kudu), Yemi Akinwonmi, shine ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar
- Wannan matakin na PDP ya biyo bayan hukuncin kotu na dakatar da shugaban PDP, Uche Secondus
Abuja - Jam'iyyar PDP ta ɗage taron kwamitin zartarwa (NWC) wanda aka tsara za'a gudanar yau Talata har sai baba ta gani, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Jam'iyyar ta ɗauki wannan matakin ne bayan hukuncin da wata kotu ta yanke na dakatar da shugaban PDP, Uche Secondus.
Secondus na cikin matsin lamba na ya yi murabus yayin da wasu kusoshin jam'iyyar suka zarge shi da nuna halin ko in kula da sauya shekar wasu saboda gazawarsa na haɗa kan yan jam'iyya.
Wane hukunci kotu ta yanke kan Secondus?
Bayan rikicin cikin gida da ya dabai-baye jam'iyyar, wata babbar kotu dake zamanta a Patakwal, a ranar Litinin ta dakatar da Secondus daga shugabancin PDP.
Mai sharii'a O. Gbasam, shine ya yanke wannan hukuncin biyo bayan karar da wasu mambobin PDP suka shigar gabansa.
Wane mataki PDP ta ɗauka bayan umarnin kotu?
A wani jawabi da ya fitar, mataimakin shugaban PDP, Yemi Akinwonmi, ya sanar da ɗage taron kwamitin zartarwa har sai baba ta gani, kamar yadda leadership ta ruwaito.
Wani sashin jawabin yace:
"Sashi na 35(3) b na kundin tsarin mulkin jam'iyyar PDP ya bani damar kira da jagorantar taron jam'iyya kasancewa babu shugaba."
"A jiya da yamma wata kotu ta bada umarnin dakatar da shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus daga kira da kuma jagorantar taron jam'iyya."
"Bisa haka, a matsayina na mataimakin shugaban jam'iyyar PDP (Kudu), ina mai sanar da ɗage taron kwamitin zartarwa da aka shirya za'a gudanar yau har sai sanarwa ta gaba."
A wani labarin kuma Ba'a Taba Shugaban Ƙasa da Ya Lalata Harkar Tsaro ba Kamar Buhari, Gwamna Ortom
Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, yace ba'a taba yin gwamnati mai muni kamar ta Buhari ba a bangaren tsaro.
Gwamnan yace shugaba Buhari ya ki maida hankali tare da baiwa ɓangaren muhimmancin da ya kamata.
Asali: Legit.ng