Sabuwar Ƙungiyar APC Ta Buƙaci Buhari Ya Zaɓi Magajinsa Daga Kudu Maso Gabas

Sabuwar Ƙungiyar APC Ta Buƙaci Buhari Ya Zaɓi Magajinsa Daga Kudu Maso Gabas

  • Wata kungiyar yan kudancin Najeriya ta APC sun bukaci Shugaba Buhari ya taimaka jam'iyyar ta bawa kudu kujerar shugaban kasa a 2023
  • Kungiyar ta yi wannan rokon ne ta bakin shugabanta, Cif Julius Ucha daga jihar Ebonyi
  • Kungiyar ta SEM ta ce an kafa kungiyar ne domin bawa sauran yan yankin kudu daman hada kai su tunkari matsalolinsu

Jihar Enugu - Kungiyar Neman Mulki ya koma Kudu, SEM, wata sabuwar kungiya a jam'iyyar APC, a karshen mako, ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da matsayinsa a jam'iyyar ya saka a zabi magajinsa daga Kudu maso Gabas a 2023.

Shugaban kungiyar kuma tsohon shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Cif Julius Ucha, daga Jihar Ebonyi, ya ce an kafa kungiyar ne don ganin samun shugaban kasa na gaba daga kudu maso gabas, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Sabuwar Ƙungiyar APC Ta Buƙaci Buhari Ya Zaɓi Magajinsa Daga Kudu Maso Gabas
Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Enugu bayan taron kungiyar, Ucha ya ce sun gano rashin yarda, tsoro, zargi a matsayin abubuwan da ke hana kudu cigaba a siyasar Nigeria, yana mai cewa za su yi aiki don ganin Ndigbo sun magance matsalolin.

Ya ce:

"Muna fatan wannan kungiyar za ta bamu daman tattaunawa kan abubuwa da suka shafi yankinmu, tare da mayar da hankali kan abubuwan da suka saka a gaba domin cimma matsayarmu."

A cewarsa, kudu maso gabas yanki ne na kasar nan mai muhimmanci don haka ya kamata a basu damar fitar da shugaban kasa domin daidaito kamar yadda The Guradian ta ruwaito.

A kan dan takarar da SEM ta fi so, Ucha ya ce:

Kara karanta wannan

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

"Dalilin kafa wannan kungiyar shine hada kan mutanen kudu, da ke neman takarar shugaban kasa, su hada kai wuri guda su fitar da mutum daya da Nigeria za ta amince da shi, muna kan hanyar cimma hakan."

Ya kara da cewa kowanne jam'iyyar siyasa a Nigeria ta san cewa lokaci ya yi da za a tsayar da dan kudu a matsayin shugaban kasa domin adalci da daidaito.

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa domin su dinke baraka

Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel