2023: Kungiyar goyon bayan Osinbajo ta fara kamfen na kasa baki daya, ta ziyarci Gwamna Masari na Katsina
- Ƙungiyoyin da ke neman Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a cikin APC suna ƙaruwa da yawa
- Daya daga cikin irin waɗannan ƙungiyoyin ita ce Progressive Consolidation Group karkashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Ahmed Mohammed
- Kungiyar, a karshen makon nan, ta ziyarci gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, don neman goyon bayansa ga Osinbajo
Katsina - Wata kungiya, karkashin inuwar Progressive Consolidation Group (PCG) ta fara nemawa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo goyon baya don zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress, APC, a zaben shugaban kasa na 2023.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa mambobin PCG a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta sun ziyarci gidan gwamnatin Katsina, domin su ja hankalin Gwamna Aminu Bello Masari don nemawa Osibanjo goyon bayan fitowa a matsayin dan takarar APC a 2023.
Shugaban kungiyar na kasa, Ahmed Mohammed, wanda ya jagoranci tawagar, ya fadawa Gwamna Masari cewa sun yi imanin Osibanjo zai kawo karshen tashin hankali tare da kawo hadin kai da kwanciyar hankali a kasar.
Ya kuma bayar da hujjar cewa kalubalen da kasar ke fama da su, na bukatar jam'iyyar ta zabi mafi cancanta don ci gaba da nasarori da manufofin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kalaman sa:
“Mun fara wayar da kan mu a fannin shugabanci na gari tun daga watan Maris na shekarar 2019, tare da kudurin hada kai don inganta babbar jam’iyyarmu, APC, don tabbatar da ganin cewa jam’iyyarmu ta sake samar da shugaban Najeriya na gaba a 2023.
"Idan aka kalli dimbin kalubalen ci gaban da kasar ke fama da su, zai zama abin hikima ne kawai jam'iyyar ta zabi Farfesa Yemi Osibanjo a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar don ci gaba da inganta ingantattun nasarori, da manufofin Shugaba Buhari."
Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa a martaninsa, gwamnan ya ba da shawarar cewa a tallata APC sosai ta yadda masu jefa ƙuri'a za su fahimci abin da jam'iyyar ta cimma zuwa yanzu da kuma dalilin da ya sa ya kamata a sake zaɓen jam'iyyar a 2023.
A cewar gwamnan, akwai manyan nasarori a karkashin gwamnatin APC a cikin shekaru shida da suka gabata ta fuskar tsaro, biyan fansho da kuma ayyukan ci gaba a kasar.
A wani labarin, tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa Adams Oshimhole, yayi magana game da zama memba na jam'iyya mai mulki da kuma wasu hujjoji game da dakatar dashi daga ofis.
Oshiomhole ya ce kotun daukaka kara ta soke dakatarwar da aka yi masa a matsayin shugaban APC, makwanni biyu bayan da aka ba da umarnin farko, PM News.
Asali: Legit.ng