2023: A karshe Tinubu ya samu daidai da shi yayin da jiga-jigan PDP suka marawa tsohon gwamna baya

2023: A karshe Tinubu ya samu daidai da shi yayin da jiga-jigan PDP suka marawa tsohon gwamna baya

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta nuna goyon bayanta ga takarar Sule Lamido a matsayin me neman shugaban kasa a 2023
  • Shugaban jam'iyyar adawar a jihar, Dr. Ibrahim Babandi ya dage cewa lallai sai Lamido ya fito neman kujerar shugaban kasa a babban zabe mai zuwa
  • A nashi bangaren, Sule Lamido ya bukaci 'yan Najeriya da su nemi zabin Allah a 2023

Jigawa - Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Bamaina da ke karamar hukumar Birnin Kudu ta Jigawa sun bukaci tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

‘Ya’yan babbar jam’iyyar adawar kasar sun bayyana haka ne a wani karamin taro da aka yi a garin Lamido a ranar Talata, 31 ga watan Agusta, jaridar PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar goyon bayan Osinbajo ta fara kamfen na kasa baki daya, ta ziyarci Gwamna Masari na Katsina

Shugaban kasa a 2023: Jam’iyyar PDP reshen Jigawa ta marawa Sule Lamido baya domin ya gaji Buhari
Jam’iyyar PDP reshen Jigawa ta marawa Sule Lamido baya domin ya zama shugaban kasa a 2023 Hoto: PM News
Asali: UGC

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Dr. Ibrahim Babandi ya dage cewa lallai sai Lamido ya shiga takarar shugaban kasa a 2023.

Dr. Bashir Jumbo, tsohon dan majalisar tarayya, shima ya bukaci Lamido da ya tsaya takarar shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce nasarorin da Lamido ya samu a matsayinsa na gwamnan jihar da kuma kwarewar diflomasiyyarsa sun sanya shi a saman duk wanda zai tsaya tseren a 2023.

Sai dai, a nasa bangaren, Lamido ya bukaci 'yan Najeriya da su nemi sa hannun Ubangiji kan zabin 'yan takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Lamido, wanda ya kuma kasance tsohon Ministan Harkokin Wajen kasar, ya ce ba daidai ba ne 'yan Najeriya su ware wani dan takara a matsayin mafi nagarta a Najeriya a 2023.

Ya ce dole ne 'yan Najeriya su fahimci cewa halin da ake ciki na bukatar sa hannun Ubangiji.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Rikicin Shugabancin PDP Ya Ƙare, an Nada Sabon Shugaba Na Kasa

Ya bukace su da su koma ga Allah don dawo da martabar da Najeriya ta rasa ta hanyar zababben dan takararta ba tare da la’akari da kabila, addini ko yankin siyasa ba.

Shugaban kasa a 2023: Dalilin da yasa bana so dan Igbo ya gaji Buhari, shahararren fasto

A wani labari, Mike Okonkwo, shugaban cocin ‘The Redeemed Evangelical Mission (TREM)’ ya yi kakkausar suka a kan ra’ayin wasu daga cikin mutanen kudu maso gabas na cewa ba za su taba gamsuwa ko samun adalci ba sai idan wani dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa.

A cikin wata hira da jaridar Guardian, Okonkwo ya bayyana cewa irin wannan tunanin kuskure ne kuma yakamata a yi watsi da shi.

Shahararren malamin addinin kirista ya kafa hujja da cewa dole ne ‘yan kabilar Igbo su gane cewa ba sai sun samar da shugaban kasa ba kafin su yi amfani da ‘yancin su na ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban Jam'iyyar PDP, Adegbola Dominic, Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel