Babban Malami Ya Bayyana Yankin da Ya Dace Ya Fitar da Wanda Zai Gaji Buhari a 2023

Babban Malami Ya Bayyana Yankin da Ya Dace Ya Fitar da Wanda Zai Gaji Buhari a 2023

  • Fasto Tunde Bakare yace arewacin Najeriya ka iya fitar da dan takarar da zai gaji Buhari a 2023
  • Bakare yace ba abun damuwa bane daga wane yanki ya fito, cancantarsa kawai ya kamata a diba
  • Faston ya kara da cewa ya kamata a jingine maganar karba-karba matukar ba tana cikin kundin mulki bane

Abuja - Shugaban coci-cocin Citadel Global Community, Fasto Tunde Bakare, yace arewa zata iya samar da shugaban ƙasan da zai gaji Buhari, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Da yake jawabi a wata fira da Channels tv, Bakare yace kowane yanki a Najeriya ka iya fitar da shugaban ƙasa matukar ya cancanta da mulkin Najeriya.

Fasto Tunde Bakare
Babban Malami Ya Bayyana Yankin da Ya Dace Ya Fitar da Wanda Zai Gaji Buhari a 2023 Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Fasto Bakare yace:

"Mu bari a fitar da nagari daga cikin nagartattu, ba abun damuwa bane ko daga wane yankin kasar nan ya fito."

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

"Na ji dukkan kace-nace da ake ta yi game da mulkin karba-karba, wasu na cewa Jonathan da Obasanjo sun shafe shekaru 14 a mulki, Buhari da Yar'adua sun yi shekara 10 sabida haka har yanzun arewa na da sauran shekara 4."
"A halin da muke ciki yanzun muna bukatar mutumin da zai iya tafiyar da mulki yadda ya kamata."

Kowace jam'iyya ta fitar da ɗan takarar ta

Bakare ya kara da cewa kowace jam'iyya ta yi iyakar bakin kokarinta wajen fitar da ɗan takara sauran kuma abarwa masu kaɗa kuri'a su tantance.

"Ya kamata jam'iyyun siyasa su fitar da yan takarar da suka dace, yan Najeriya su zabi wanda yafi cancanta. Ko mulkin ya tafi yankin kudu ko arewa kujera ɗaya ce dai."
"Idan inyamuri ne ya zama, idan Bayerabe ne ya zama, idan ma ɗan arewa ne, Bahaushe ko bafullatani, mubar shi ya zama, ina faɗin wannan har cikin zuciyata."

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Shin akwai mulkin karba-karba a kundin mulki?

Babban malamin yace idan mun yi wa juna alkawarin karba-karba to ba laifi bane muyi hakan, amma idan babu tsarin a kundin tsarin mulki, to kamata ya yi mu watsar da shi mu fuskanci abinda ya dace.

Ya kara da cewa yankin da mutumin ya fito ba shine abin kallo ba, ingancin shi da abinda zai iya yi ga yan Najeriya shine ya kamata a maida hankali.

A wani labarin kuma Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno yace yan Boko Haram sun kai masa hari sama da 50

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa manema labarai a fadar gwamnatin tarayya bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata.

Zulum yace sama da mutum 100,000 ne aka kashe a cikin shekaru 12 da aka kwashe na rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262