Da Duminsa: Kotu Ta Maida Uche Secondus Mukaminsa Na Shugaban Jam'iyyar PDP

Da Duminsa: Kotu Ta Maida Uche Secondus Mukaminsa Na Shugaban Jam'iyyar PDP

  • Wata babbar kotu a jihar Kebbi ta soke umarnin dakatarwa, tace Uche Secondus ya koma kan kujerarsa ta shugaban PDP
  • Alkalin kotun, mai shari'a Nusrat Umar, itace ta bayyana haka bayan ta saurarin karar a Birnin Kebbi
  • Wannan umarnin na zuwa awanni kaɗan bayan jiga-jigan PDP sun yanke hukuncin ɗora shugaban riko

Abuja - Wata babbar kotu a jihar Kebbi ta bada umarnin cewa Prince Uche Secondus ya koma matsayinsa na shugaban jam'iyyar PDP na kasa, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Alkalin kotun, Mai shari'a Nusrat Umar, ita ce ta bada wannan umarnin bayan shigar da kara gabanta a Birnin Kebbi, babbar birnin jihar.

A karar da aka shigar gaban kotun, wadda akaiwa lamba KB/AC/M. 170/2021, mai shari'a Nusrat tace ta gamsu sosai bayan karanta rantsuwar wanda ake karewa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An kammala bincike kan DCP Abba Kyari, IGP ya karbi rahoton

Shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus
Da Duminsa: Kotu Ta Maida Uche Secondus Mukaminsa Na Shugaban Jam'iyyar PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Umarnin kotu kan Secondus

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umarnin da kotun ta bayar yace:

"Kotu ta bada umarnin wanda aka shigar kara na farko, Uche Secundus, ya cigaba da aikinsa na shugabancin jam'iyyar PDP ta kasa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Najeriya (1999 wanda aka yiwa garambawul)"
"Da kundin dokokin jam'iyyar PDP yayin da za'a cigaba da sauraron karar har zuwa hukuncin karshe."
"Wannan kotu ka iya sake bada wani umarnin idan bukatar hakan ta taso nan gaba."

Wasu mambobin jam'iyyar PDP, Yahaya Usman, Abubakar Mohammed da kuma Bashar Suleman, sune suka shigar da kara gaban kotu.

Punch ta ruwaito cewa rikicin cikin gida ya mamaye jam'iyyar PDP yayin da wasu manyan masu faɗa a ji a jam'iyyar suke neman a tsige Secondus.

PDP ta naɗa mukaddashin shugaba

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa PDP ta kawo karshen rikicin shugabanci da ya taso bayan kotu ta dakatar da Uche Secondus

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Bayan dakatar da Secondus, mutane biyu sun yi ikirarin cewa sune shugabannin jam'iyyar wadda hakan ya janyo rikici.

Sai dai daga karshe, mahukunta a jam'iyyar sun yi taro a ranar Alhamis sun amince da nadin Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaba.

A wani labarin kuma Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa yanzun babu sauran wani ɗan bindiga a jihar Kebbi

Gwamnan yace a halin yanzun sai dai yan bindiga su zo daga makotan jihohi su aikata ta'addanci su koma.

Gwamnan ya kuma jinjina wa jami'an tsaro bisa jajircewarsu tare da alkawarin samar musu da abinda suke bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel