Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, Ya Fadi Abinda Ka Iya Faruwa da Yan Najeriya a 2023

Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, Ya Fadi Abinda Ka Iya Faruwa da Yan Najeriya a 2023

  • Tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole, yace Allah na tare da yan Najeriya yayin da 2023 ke kara kusantowa
  • Oshiomhole yace shi a karan kansa yana fatan alheri ga Najeriya a koda yaushe kuma ba ya jin tsoron komai
  • Ya kara da cewa mutane na ta maganar tsoron wani abu, amma a wajensa fatan alheri yake yi wa yan Najeriya

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, ranar Asabar, yace yana fatan Allah ba zai bar yan Najeriya cikin matsala ba yayin da zaɓen 2023 ke kara gabatowa, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Oshiomhole ya faɗi haka ne a wurin bikin rantsar da Victoria Unoarumi a matsayin shugabar Rotary Club Abuja.

Yace ba wai ya shiga APC don ya zama shugabanta bane, sai don a kafa wata jam'iyya mai karfi da zata yi waje da PDP daga madafun iko, kamar yadda punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Siyasa: Ina Nan Daram a Kan Kujerata, Shugaban PDP Ya Maida Martani

Adams Oshiomhole, tsohon shugaban APC
Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, Ya Fadi Abinda Ka Iya Faruwa da Yan Najeriya a 2023 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Tsohon shugaban yace:

"Ina fata nagari ga Najeriya, amma bana jin tsoron wani abu da ka iya faruwa a 2023, mutane na magana kan tsoro amma a wajena koda yaushe ina fatan alheri ne. Ina tunanin zuwa 2023, Allah ba zai kyale kasar dake dauke da mutum miliyan 200m ba."
"Demokaradiyya ta samu gindin zama a mulkin jam'iyyar mu, ba ta kai can kololuwa ba, amma abu kaɗan za'a gyara komai."
"Ina da yakinin cewa, Allah zai taimaki Najeriya ta cigaba da zama cikin kyakkyawan mulkin demokaradiyya a 2023."

Oshiomhole ya kara da cewa a koda yaushe ya kalli yawan matsalolin da suka baibaye Najeriya, tunanin dake zuwa masa shine Najeriya tafi karfin dukkansu.

Meyasa Oshiomhole ya fita harkar shugabancin APC?

Mista Oshiomhole yace:

"Ba wai makon da ya gabata aka yanke hukuncin cire ni daga ofishin shugaban jam'iyya ba, tun 2 ga watan Yuli, 2020, mako biyu bayan an tsige ni daga Ofis."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

"Dalilin da yasa na yi wannan maganar shine naga wasu na maganar cewa mutane ba su ma san an yi watsi da lamarin ba."
"Nayi jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan cire ni, inda nace ba tare da duba anbi doka ko ba'a bi ba wajen tsige ni, na amince da kyakkyawan niyya kuma na yi alkawarin ba zan sake neman kujerarar ba."

Ya kuma kara da cewa zai cigaba da zama mamba a jam'iyyar APC kuma zai taimaka wa jam'iyyar dai-dai gwargwado.

A wani labarin kuma Mutum uku sun mutu yayin da miyagun Yan bindiga suka kai sabon hari jihar Kaduna

Wasu gungun yan bindiga sun kai sabon hari kauyukan dake yankin karamar hukumar Zangon Kataf, Kudancin Kaduna.

Lamarin ya faru ne a kauyen Machun da kuma Manuka, inda akalla mutum uku suka mutu wasu suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel