Shugaban kasa a 2023: Dalilin da yasa bana so dan Igbo ya gaji Buhari, shahararren fasto

Shugaban kasa a 2023: Dalilin da yasa bana so dan Igbo ya gaji Buhari, shahararren fasto

  • Mike Okonkwo na cocin ‘The Redeemed Evangelical Mission’ ya bayyana ra'ayinsa game da neman shugabancin Igbo
  • Babban faston ya ce akwai kuskure a fadin cewa sai dai idan dan kudu ne ya zama shugaban kasa, 'yan kabilar Ibo ba za su samu adalci ba
  • Okonkwo ya ce maimakon haka kamata yayi ace 'yan Najeriya, musamman 'yan kudu maso gabas, suyi tunani sosai game da canza tsarin abubuwa na yanzu

Mike Okonkwo, shugaban cocin ‘The Redeemed Evangelical Mission (TREM)’ ya yi kakkausar suka a kan ra’ayin wasu daga cikin mutanen kudu maso gabas na cewa ba za su taba gamsuwa ko samun adalci ba sai idan wani dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa.

A cikin wata hira da jaridar Guardian, Okonkwo ya bayyana cewa irin wannan tunanin kuskure ne kuma yakamata a yi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Ba boye-boye: Mu ‘yan siyasa ne muka jefa kasar a cikin matsala – Rochas Okorocha

Shugaban kasa a 2023: Dalilin da yasa bana so dan Igbo ya gaji Buhari, shahararren fasto
Malamin ya ce dole a sauya abubuwa a Najeriya
Asali: UGC

Shahararren malamin addinin kirista ya kafa hujja da cewa dole ne ‘yan kabilar Igbo su gane cewa ba sai sun samar da shugaban kasa ba kafin su yi amfani da ‘yancin su na ‘yan Najeriya.

Okonkwo ya bayyana cewa baya son wani dan yankin gabas mai wannan tunanin kuma a karkashin wannan tsarin na yanzu ya sami shugabanci saboda a cewarsa, abubuwan da ke faruwa a yanzu ba za su iya kawo canjin da ake so ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya

A wani labari, wani tsohon jakadan Najeriya zuwa Malysiya, Ambasada Yerima Abdullah, ya yi kira ga masu rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara suyi nazari kan illar ballewar Najeriya.

Abdullahi, wanda makusancin Buhari ne, ya ce zai fi kyautata masu rajin su nemi zaben raba gardama saboda hakan zai fi kyau don zaman lafiya da cigaban kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Abdullahi ya bayyana illar da ballewa za ta yiwa yan kasuwan Igbo saboda suna baje a dukkan sassan kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel