Da Dumi-Dumi: Gwamna Ya Rushe Majalisar Zartarwar Jiharsa, Ya Sallami Kowa

Da Dumi-Dumi: Gwamna Ya Rushe Majalisar Zartarwar Jiharsa, Ya Sallami Kowa

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da rushe baki ɗaya masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa
  • Gwamnan ya faɗi hakane a wurin taron gaggawa da ya kira a faɗar gwamnatinsa dake Lafia
  • Kwamishinan shari'a ya yi jawabin godiya a madadin baki ɗaya tsofaffin ma'aikatan bisa damar da ya ba su

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya rushe majalisar zartarwa na jiharsa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya rantsar da kwamishinonin da ya sallama ne a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2019.

Gwamnan ya sanar da wannan matakin ne yayin wani taron gaggawa na mambobin majalisar zartarwa da ya kira, wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar dake Lafia ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamnan APC na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa
Da Dumi-Dumi: Gwamna Ya Sallami Dukkan Yan Majalisar Zartarwa a Gwamnatinsa Hoto: today.ng
Asali: UGC

Gwamna Sule ya sanar da sallamar kwamishinoni, masu bashi shawara, da manyan masu bashi shawara ta musamman banda waɗanda ke jagorantar ɓangaren ayyukan jin kai.

Sule ya yi amfani da damar da ya samu wajen gode musu bisa sadaukarwarsu wajen aiki tukuru a lokacin da suke cikin ofis a gwamnatinsa.

Tsaffin mambobin sun gode wa gwamna

Da yake martani a madadin tsofaffin mambobin kwamitin zartarwa, Abdulkarim Abubakar, wanda kafin lokacin shine kwamishinan shari'a ya yi godiya ga gwamna bisa damar da ya basu a gwamnatinsa.

Ya kuma tabbatarwa gwamna Sule cewa zai cigaba da samun cikakken goyon bayansu yayin da ake fuskantar babban zaɓe a 2023.

Wane dalili yasa gwamnan ya ɗauki wannan matakin?

Wani babban jami'in gwamnatin Nasarawa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace mafiyawancin waɗanda gwamnan ya sallama sun shiga gwamnatin ne bisa shawarar magabata.

Kara karanta wannan

An saki Matar da ta kashe mijinta a Kano bayan shekaru 7 a Kurkuku

Hakan yasa ake zargin suna boye namijin kokarin da gwamnan yake yi a zamanin mulkinsa.

Yace:

"Ya zama tilas gwamna Sule ya sallamesu domin ya samu damar gina gwamnatinsa yadda yake so."
"Matukar Sule bai ɗauki matakin da ya dace ba, to yana iya rasa tikitin takara a karo na biyu."
"Ina da tabbacin ya yi hakane domin samun cikakken iko a gwamnatinsa yayin da yake kokarin neman zarcewa kan kujerarsa a zaɓen 2023."

A wani labarin kuma Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Zata Samar Wa Matasa Masu Digiri 20,000 Aikin Yi Mai Tsoka

Ana tsammanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai yi wata sanarwa dangane da wani shiri na musamman na matasa masu digiri ranar Talata.

FG ta kirkiri shirin ne da nufin samarwa matasa yan Najeriya da suka kammala digiri 20,000 aikin yi a wasu ɓangarorin gwamnati da kamfanoni a faɗin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel