Lalong ya rufe majalisar jihar Filato don hana tsige shi? Gwamnan ya bayyana gaskiyar lamari
- Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong yana fuskantar tuhuma kan zargin aikata manyan laifuka don kaucewa tsigewa
- Wasu mutane na zargin Lalong ya yi amfani da wasu 'yan sanda masu makamai wajen rufe majalisar dokokin jihar
- Amma gwamnatin ta musanta wannan ikirari, inda ta dage cewa gwamnan ba ya tsoma baki a harkokin majalisa
Filato - Gwamnatin Filato ta mayar da martani kan ikirarin cewa Gwamna Simon Lalong ya rufe majalisar dokokin jihar don hana fara aiwatar da yunkurin tsige shi.
Akwai rahotanni daga Channels TV da The Sun cewa wasu jami'an tsaro dauke da makamai sun kewaye harabar Majalisar saboda rikicin da ka iya tasowa daga ci gaba da kiran a tsige Lalong.
Sai dai gwamnatin ta musanta ikirarin cewa gwamnan ne ya aike da jami’an tsaron don rufe ginin a ranar Litinin 30 ga watan Agusta.
Da yake musanta ikirarin, kwamishinan labarai da sadarwa, Dan Manjung, ya ce karya ce kuma ya kamata a yi watsi da su, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Manjung ya bayyana cewa kakakin majalisar, Honorabul Abok Nuhu Ayuba ne ya gabatar da rahoton a ranar Litinin.
Kwamishinan ya kara da cewa Lalong ba shi da masaniya kan abin da ya faru a harabar kuma baya cikin dabi'ar shi shiga cikin harkokin sauran bangarorin gwamnati.
Don bayanan, ya ambaci cewa gwamnan shine na farko a cikin takwarorinsa da ya aiwatar da cikakken cin gashin kan majalisar a Filato.
Rikicin Jos: An tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato
A baya mun kawo cewa an tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato a safiyar ranar Litinin. Ponven Wuyep, magatakardan majalisar ya tabbatar da cewa an kara yawan jami'an tsaro amma kuma ana cigaba da aiwatar da sha'anonin mulki.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya musanta rade-radin da ke yawo na cewa an garkame majalisar jihar baki daya.
A ranar Asabar, a yayin taron manema labarai, majalisar ta bukaci jama'ar jihar da su bai wa kan su kariya bayan rikicin da ke aukuwa a jihar a cikin kwanakin nan.
Asali: Legit.ng