Siyasar Najeriya
A ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024, mazauna jihar Ondo za su fita akwatunan zaɓe su zaɓi wanda suka ga ya dace ya shugabance su a matsayin gwamna.
Akwai manyan 'yan takara 4 a zaben gwamnan Ondo na 2024,: Lucky Aiyedatiwa (APC), Ajayi Agboola (PDP), Otunba Bamidele Akingboye (SDP), da Sola Ebiseni (LP).
Gwamnatin jihar Ondo karkashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ta ayyana ranar hutu domin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar Asabar.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya nuna cewa Atiku Abubakar, ba zai samu tikitin takarar shugaban kasa ba na PDP a zaben 2027.
Sa'o'i 24 gabanin fafata zabe, kotun ɗaukaka kara ta kori ɗan takarar gwamna na jam'iyyar LP, Chief Olusola Ebiseni, ts yu fatali da hukuncin babbar kotun tarayya.
Ana zargin Oba Kayode Adenekan Afolabi a jihar Osun kan kiran mambobin PDP su kai farmaki kan yan jam'iyyar APC a cikin wani faifan bidiyo inda ya musanta.
Sanata Kawu Sumaila ya bukaci shugaban NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa ya fito baiat jama'a ya janye zargin da ya masa kuma ya ba shi hakuri cikin awanni 24.
A karo na biyu, Majalisar jihar Delta ta sake dakatar da mambanta, Hon. Oboror Preyor daga jam'iyyar PDP da ke wakiltar mazabar Bomadi kan nuna rashin da'a.
Sabon gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya rusa shugabancin hukumomin gwamnati, ya sallami masu riƙe da muƙaman siyasa gaɓa ɗaya bayan shiga ofis.
Siyasar Najeriya
Samu kari