Siyasar Najeriya
Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum.ya ce har yanzun PDP ce a sahun gaba a tsagin adawa kuma dole sai da ita za a iya mukushe APC a zaɓen 2027.
Rikicin sarautar Kano, hadin kan 'yan siyasa musamman 'yan jam'iyyar adawa da kudirin haraji na cikin manyan abubuwan da za su cigaba da jan hankali a 2025.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya ce ikirarin da APC ta yi cewa ya ciyo bashin kusan Naira biliyan 100 a asirce karya ce da ba ta da tushe ballantana makama.
Hon. Udeh Okoye ya kama aiki a matsayin sabon sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wanmdda ta sauke Sanata Samuel Anyanwu.
Kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya ta nuna damuwa kan rigimar siyasar da ke aukuwa a jihar Benuwai, ta bukaci SGF Sanata George Akume ya canza salo.
Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya halarci wurin taron rabon kayan tallafi na wani ɗan majalisar tarayya na LP, ya ce babu gaba ko ƙiyayya a siyasa.
Rikicin siyasa ya kara kaurewa tsakanin Shehu Sani, Nasir El Rufa'i da Reno Omkri kan yadda Bola Tinubu ke tafiyar da mulki. Yan siyasar sun harbin juna da kalamai.
Kakakin kungiyar matasan jam’iyyar PDP na kasa, Dare Glintstone Akinniyi, ya bayyana shirin jam’iyyar na sauke Tinubu da APC daga mulki a zaben 2027.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya yi magana kan batun da aka rika yadawa kan cewa ya cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi.
Siyasar Najeriya
Samu kari