Siyasar Najeriya
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya sake tarbar jagororin jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano zuwa APC bayan sun sauya sheka.
An kawo jerin wasu malaman da za su iya goyon bayan Bola Tinubu a 2027. Ana ganin cewa irinsu Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingirza su sake talla Tinubu a 2027
Elebute-Halle, tsohuwar ƴar takarar gwamna a inuwar ADP a jihar Ekiti, ya jagoranci dubban magoya bayanta zuwa APC, ta ce sun gamsu da mulkin Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya ce yana kwarewar zama shugaban ƙasa kuma da yiwuwar ya nemi takara idan Bola Tinubu ya hakura da neman tazarce.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce lokacin tsayawa nuna adawa da sukar juna ya wuce, ya kamata su Atiku da Obi su shigo a tafi tare don ceto ƴan Najeriya daa ƙunci.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar Alhamis ya bayyana cewa za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025.
NNPP ta bayyana shirinta na haɗa maja da duk jam'iyyar da ta shirya domin karɓe mulki daga jam'iyyar APC a zaben 2027, ta gano wani shirin da APC ke yi.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Cif Bode George, ya bayyana cewa hakurin da Shugaba Tinubu ya ba shi ya sanya ya ki barin Najeriya.
Zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya koka kan yadda gwamnatin Hodwin Obaseki ke ci gaba da karbo basussuka yayin da ake shirin mika masa mulki.
Siyasar Najeriya
Samu kari