Siyasar Najeriya
Jarumar Kannywood kuma hadimar gwamnan jihar Kano, Asma'u Abdullahi, ya fice daga jam'iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya. Asma'u ta koma jam'iyyar APC.
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayyana cewa yana da yaƙinin cewa ya zarce alƙawurran da ya ɗaukarwa mutane a lokacin yakin neman zabe a 2016.
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan tsare-tsaren da ta kawo na tattalin arziki. Atiku ya ce an yi masa fashin kuri'u a zaben 2023 da ya gabata.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe ya ce Shugaba Bola Tinubu na yin abin da ya dace kuma ƴan Najeriya za su kara ba shi dama a babban zaben 2027.
APC ta ce ba ta jefa PDP cikin rikicin cikin gida ba a Najeriya. APC ta ce gwamnan PDP ya mayar da hankali wajen kawo cigaba maimakon zargin APC.
Yayin da ya rage ƴan kwanaki a fita zaɓen gwamna a jihar Ondo, tsohon ɗan majalisar tarayya da wasu manyan ƙusoshin PDP sun haɗe da Gwamna Aiyedatiwa a APC.
Jam'iyyar APC mai mulki ta mayar da martani da Gwamna Seyi Maminde na jihar Oyo wanda bisa dukkanin alamu ya fara shirin neman karawa da Tinubu a 2027
Za a ga jerin APC da aka ji sun soki gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya. Alal misali, sukar gwamnatin Bola Tinubu ne ya jawo Muhammad Ali Ndume ya rasa matsayinsa.
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Isaac Fayose ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa ya yi kudi ne lokacin da Ayodele Fayose ke mukin jihar inda ya ce shi ɗan kasuwa ne.
Siyasar Najeriya
Samu kari