Siyasar Najeriya
Mai shari'a James Omotosho na babbar kotun tarayya ta soke matakin tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya mayar da shi kan muƙaminsa.
Sanata Tahir Mungono daga jihar Borno ya zama sabon mai tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya bayan APC ta sauke Muhammed Ali Ndume yau Laraba.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya jawo ƙarin mutane cikin gwamnatin jihar, ya fitar da sunayen mutane 1,270 da naɗa a matsayin masu taimaka masa.
Majalisar dattawan Najeriya ta sauke Sanata Ali Ndume daga matsayin babban mai ladabtarwa na majalisar bayan sukar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sha alwashin sake kwato kujerun shugabbancin da ta rasa a hannun jam'iyyun siyasa. Ta shirya dawowa kan mulki.
Kansilolin karamar hukumar Egor a jihar Edo sun tsige shugaban karamar hukumar kan zarge-zargen rashawa. Sun kama shi da kara kasafin kudi da N1.7bn.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ta ce ta kammala duk wasu shirye-shirye na gudanar da zaɓen kananan hukumomi a ranar 19 ga watan Oktoba, 2024.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya umurci shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 18 da kansilolin gundumomi 33 na jihar da su kama aiki.
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osobo ya bayyana yadda ya yi mu'amala da tsohon shugaban soji a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a 1985.
Siyasar Najeriya
Samu kari