Siyasar Najeriya
Yayin da rikicin shugabancin LP ke ƙara tsananta. ɓangaren Julius Abure ya dakatar da Gwamna Alex Otti na jihar Abia da wasu ƴan Majalisa 5 bisa zargin cin amana.
Shugaban kungiyar ciyamomi ta kasa watau ALGON reshen jihar Legas, Kolade Alabi ya yanke jiki ya faɗi yana tsaka da yin jawabi a taron masu ruwa da tsakin APC.
Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya tabbatar da sauya shekarsa daga NNPP zuwa APC a wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa ya karanta yau Laraba.
Jam'iyyar SDP ta karbi wasu matasa a jihar Kano. Galibin matasan sun fito ne daga jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano. 'Yan jam'iyyar AA sun koma SDP a Imo
Wani jigon APC a jihar Ribas, Eze Chukwuemeka Eze ya bayyana cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne mafita a Najeriya domin zai iya maganxe matsaloli.
Majalisar wakilai za ta kafa kwamitin sulhu tsakanin Simi Fubara da Nyesom Wike a jihar Rivers. Majalisar za ta saka dattawan Najeriya a kwamitin sulhun.
Abdullahi Ganduje ya ce APC za ta karɓi Rabi'u Musa Kwankwaso idan ya dawo, yana mai cewa za su taimaka masa domin kar siyasarsa ta mutu murus a inda yake.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyaja cewa ba zai fice daga PDP ba a yanzu amma zai jagoranci kawancen da zai kawo karshen APC.
Karamin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ba su maraba da Rabiu Musa Kwankwaso a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Siyasar Najeriya
Samu kari