Siyasar Najeriya
Majalisar wakilai ta fara muhawara kan shirin dawo da zaben shugaban kasa, gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da na jihohi a rana daya a zaben 2027.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigo a jam'iyyar PDP mai adawa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zabe a bababn zaben 2027.
Jam'iyyar SDP ta ce ta sallami Nasir El-Rufa'i daga harkokinta har zuwa shekara 30 masu zuwa. SDP ta ce El-Rufa'i bai taba rajista da ita duk da ikirarin da yake yi.
A labarin nan, za a ji cewa Farfesa T. A Muhammad Baba ya ɗora alhakin taɓarɓarewar yankin Arewa a kan sakaci da barin shugabanni suna abin da suka ga dama.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan hadakar 'yan adawa. Ya nuna cewa yayin da suke ta shirye-shirye, ita ma APC na yin na ta shirin.
Wata kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu a Kudu maso Gabas ta tara wa Tinubu miliyan 200 domin sayen fom din takara a zaben 2027 mai zuwa.
Jam'iyyar NNPP ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya daina tankawa Rabiu Musa Kwankwaso. Ta ce so yake ya yi a rika kula shi don ya yi suna.
Jam'iyyar ADC reshen jihar Benue ta fito ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamna Hyacinth Alia na jihar ke daukar nauyinta. Ta ce ba gaskiya ba ne.
Wani jigo a jam'iyyar PDP, Umar Sani, ya kawo dalilan da suka sanya ya kamata yankin Arewa ya fi dacewa ya marawa Goodluck Jonathan fiye da Peter Obi baya a 2027.
Siyasar Najeriya
Samu kari