Siyasar Najeriya
Sanata Ned Nwoko ya ce APC a ƙarƙashin Tinubu za ta ƙirƙiri Jihar Anioma, maganar da Ganduje ya gasgata yana mai cewa shugaban kasa ya goyi bayan kudurin.
Gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP sun bayyana cewa ba su da shirin shiga hadakar jam'iyyun adawa domin tunkarar babban zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Daruruwan 'yan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa LP a Abia, bisa jagorancin Hon. Ojo, wanda ya ce PDP ta mutu murus a jihar. LP ta ce yanzu ta kara samun karfi.
Shugabannin APC da NNPP a mazabar Kargi a karamar hukumar Kubau sun koma jam'iyyar SDP. Ana ganin hakan na cikin tasirin Nasir El-Rufa'i a jihar Kaduna.
Jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Delta, sun bayyana cewa ba su gayyar Gwamna Sheriff Oborevwori zuwa cikin jam'iyyar. Sun nuna cewa ya ci gaba da zamansa a PDP.
Yayin da 2027 ke karatowa, ‘yan siyasa na kokarin janyo Buhari cikin tafiyarsu, inda suke kai masa ziyara don neman goyon baya da tasirinsa a siyasar Arewa.
Jam'iyyar APC reshen jihar Borno ta yi kira da babbar murya ga shugaban kasa kan Kashim Shettima. Ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da tafiya da shi.
Jagoran 'yan Neja Delta, Thomas Ekpemupolo Tompolo ya ce yana kokarin sansanta rikicin jihar Rivers tsakanin Simi Fubara da Wike. Ya ce Fubara zai dawo kujerarsa.
Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya yi zargin cewa Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu da shirin ficewa daga jam'iyyar APC.
Siyasar Najeriya
Samu kari