Siyasar Najeriya
Tsohon ministan muhalli da ya yi aiki a gwamnatin Muhammadu Buhari, Mohammed Abdullahi ya sauya sheka daga APC. Ana cewa zai yi takara a zaben 2027.
A labarin nan, za a ji cewa kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta ce babu wani katabus da gwamnatin Tinubu ta tabuka a cikin shekaru biyu da ta yi tana mulki.
Dr. Lamido ya nemi Kudu maso Yamma su fitar da dukkan ‘yan takarar shugaban kasa a 2027, sannan a bai wa Kudu maso Gabas dama a 2031 don adalci da daidaito.
Hukumar INEC ta sanar da cewa za a yi zaben gwamnoni a jihohin Ekiti da Osun a Yuli da Agusta a 2026. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka.
Hon. Bamidele Salam da Hon. Oluwole Oke sun yi cacar baki kan zargin cewa APC na zawarcin gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, don ya bar PDP kafin 2026.
A wannan labarin, za a ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya goyi bayan karawa mata gurbi a majalisun jihohi da tarayya.
Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya sake nuna alamun da ke tabbatar da shirinsa na komawa jam'iyyar APC, ya ce yana kaunar PDP amma lokaci ya yi da zai motsa.
'Yan majalisar tarayya daga jihar Cross River sun amince da tazarcen shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda ayyukan da ya fara. Sun goyi bayan tazarcen Bassey Otu.
Tsohon shugaban PDP reshen jihar Oyo, Kunmi Mustapha, ya bayyana cewa Gwamna Seyi Maminde ya nuna cewa ya cancanci zama shugaban ƙasa idan aka duba ayyukansa.
Siyasar Najeriya
Samu kari