Siyasar Kano
Rashin gayyatar Abba Kabir ko Rabiu Kwankwaso da Kawu Sumaila ya yi zuwa bikin auren 'ya'yansa ya bar baya da kura inda yan NNPP ke zargin zai iya komawa APC.
Shugaban karamar hukumar Kumbotso, a jihar Kano, ya dauki nauyin dalibai 1,100, ya kaddamar da gyaran makarantu, rabon kayan karatu, da tallafawa matasa.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware N33.45bn domin gudanar da wasu muhimman ayyukan ci gaba ga al'umma a faɗin jihar.
Sanata Barau ya karɓi shugabanni da matasa daga NNPP zuwa APC, inda suka bukaci gyaran madatsar ruwa, kasuwa da kammala ofishin ‘yan sanda a Getso.
Fitaccen jarumin Kannywood, Mustapha Badamasi Nabraska ya sauya sheka zuwa APC bayan fita daga NNPP da Kwankwasiyya a hannun Sanata Barau Jibrin a Abuja.
Babbar kotun Kano ta tabbatar da ƴancin kananan hukumomin jihar 44, ta ba ɗa umarnin ci gaba da sakar masu kuɗaɗensu kai tsaye ba tare da wata tangarɗa ba.
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje, ya ce Arewa ta hakura da takarar 2027, amma wasu manyan yankin sun ce wannan matsayi barazana ce ga tsarin dimokuradiyya.
APC na shirin kafa gwamnatin basaja a Kano don sa ido kan ayyukan Gwamna Yusuf, tare da gabatar da rahotanni da shawarwari na inganta tafiyar da mulki.
Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano (REMASAB) kuma sanannen dan siyasa, Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya yi bankwana da duniya bayan fama da jinya.
Siyasar Kano
Samu kari