Siyasar Kano
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau murnar cika shekara 70 a duniya, ya tuna gudummuwar da ya bayar.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya sanar da fita daga NNPP da Kwankwasiyya zuwa APC a Kano tare da goyon bayan Tinubu.
'Yan sanda sun tsare wasu matasa biyu yan NNPP bisa zargin taba kimar shugaban karamar hukumar Tofa, Hon. Yakubu Ibrahim Addis a shafin Facebook.
Tafiyar Kwankwasiyya ta samu karuwa da wasu mambobin APC akalla 100 a yankin karamar hukumar Kibiya, suka sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP a Kano.
Shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce jam’iyyar su za ta hana Gwamna Abba Yusuf dawowa kan mulkin Kano a 2027, koda me zai faru.
A labarai nan, za a ji cewa mutanen Kwankwasiyya akalla 1000 suka bayyana cewa ba za su iya ci gaba da zama a NNPP ba bayan sun hango alheri a APC.
Wasu yan Kwankwasiyya a kananan hukumomin Dala, Fage da Ungoggo a Kano sun sauya sheka daga NNPP zuwa APC, sun ce sun gamsu da manufar Shugaba Tinubu.
A labarin nan, za a ji cewa 'yar jam'iyyar hamayya a Kano, Badariyya Garko ta zayyano ayyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai yankinta na Garko.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da sauran wadanda ake tuhuma a kotu sun kawo tsaiko a zaman ranar Litinin.
Siyasar Kano
Samu kari