Siyasar Kano
Jam'iyyar APC ta fara fuskantar rikici a Kano bayan sauya shekar Abba Kabir Yusuf. Bangaren Barau Jibrin da Abdullahi Ganduje sun yi taro daban-daban maimakon haduwa
Dr. Yusuf Bello Danbatta ya kare Gwamna Abba Yusuf, inda ya ce bai ci amanar Kwankwaso ba. Ya ce sauya sheka al'ada ce a siyasar Kano da Kwankwaso ya fara.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi 'yan Kwankwasiyya mazauna Dubai a tafiye-tafiye da ya yi zuwa kasar waje. Ya yi magana kan sauya shekar Abba Kabir.
Dr. Yusuf Bello Danbatta ya yi sharhi kan sauya shekarar Gwamna Abba Yusuf zuwa APC. Ya ce "ba a sarki biyu a gari ɗaya" don haka Abba ya bar Kwankwasiyya.
Kungiyar mabiyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da aka fi sani da Kwankwasiyya ta jinjinawa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo da sauran yan amana.
Uwargidan tsohon gwamnan Kano, Hafsat Ganduje, ta bukaci Rabiu Kwankwaso da ya janye gabar siyasa, domin ci gaban Jihar Kano tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Majalisar dokokin Kano ta bayyana cewa labarin da ake yadawa cewa ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo daga mukaminsa ba gaskiya ba ne.
Bangaren jam'iyyar NNPP da Agbo Major ke jagoranta ya bayyana cewa Kwankwaso ba dan jam'iyya ba ne a lokacin zaben 2029, ta nesanta kanta daga kalmansa.
An samu rashin fahimtar juna a taron jam'iyyar APC a jihar Kano. Wannan shi ne taron farko da ya hada 'yan bangaren Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Ganduje.
Siyasar Kano
Samu kari