Siyasar Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan ya yi murabus daga NNPP. Gwamnan ya yi muhimman nade-nade bayan shiga APC.
Gwamna Abba Yusuf ya nada shugaban hukumar alhazai, ya kara wa jaruma Aina’u Ade girma, yayin da ya nada Rahama shugabar cibiyar yaki da rashawa a Kano.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi Baƙuncin Mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidansa da ke Abuja.
Sanata Hanga ya umarci tsofaffin shugabannin NNPP su dawo da motocin da ya ba su bayan sauya sheka zuwa APC a Kano; AA Zaura ya yi alkawarin ba su wasu sababbi.
Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta karyata cewa tana cikin rudani game da masu mata takara a zaben cike gurbi a majalisar dokokin jihar Kano da za a yi.
Mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Gwarzo ya halarci saukar karatun Alkur'ani a daidai lokacin da aka fara kiraye-kiraye ya yi murabus daga mukaminsa.
Kwamishiniyar harkokin mata da yara a Kano, Hajiya Amina Sani (Amina HOD), ta fice daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya tayar da kura a siyasar jihar.
Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa ficewar Abba Kabir zuwa APC babban butulci ne ga Rabiu Kwankwaso, yana mai cewa gwamnan zai fadi a zaben 2027.
Kwamishinan yada labarai a Kano ya ce rikicin cikin gida ya lalata NNPP, yana mai cewa canjin tambari daga kwandon kayan marmari zuwa littafi ne ya haddasa matsala.
Siyasar Kano
Samu kari