Dalilim da Ya Sa Aka Fara Shakku kan Sahihancin Zaben da INEC Ta Gudanar a 2023
- Tsohon kwamishinan INEC, Mike Igini, ya yi hasashen dalilin da ya sa yan Najeriya suka daina amincewa da hukumar zaben Najeriya
- Ya ce gazawar hukumar INEC wajen tura sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ta intanet na 2023 ta sa jama’a suka rasa amincewa da ita
- Igini ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan matsalar fasaha da INEC ta ce ta fuskanta ba, duk da cewa ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Mike Igini, ya hango abin da ya ke tunanin ya jawo yan Najeriya suka daina amincewa da hukumar zabe.
Ya ce gazawar hukumar INEC wajen tura sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 intanet ta raunana amincewar jama’a da ita, lamarin da ya jawo rashin yarda da hukumar a tsakanin al’umma.

Source: Twitter
Igini ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels TV.
Ya ce duk da kasancewarsa tsohon kwamishinan zaɓe, har yanzu ba zai iya yin cikakken bayani kan ainihin matsalar fasaha da hukumar ta ce ta fuskanta a lokacin zaɓen ba.
Dalilin shakkun yan Najeriya kan INEC
Ya ce na’urar BVAS ta yi aiki, amma gazawar tura sakamakon ta intanet a ɗaya daga cikin zaɓuka uku da aka gudanar a rana guda ta sa jama’a suka rasa amincewarsu da INEC.
Igini ya ce:
“A zaɓen 2023, me ya yi aiki, kuma me ya karya amincewar jama’a? Na’urar BVAS ta yi aiki amma abin da ya karya amincewar jama’a, shi ne cewa an gudanar da zaɓuka uku a rana guda, amma zaɓe guda ɗaya ne kawai aka kasa tura sakamakonsa, wato zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
"Ba zai yiwu mu koma baya ba," Gwamna ya yi fatali da yunkurin dawo da tallafin Fetur
“Wannan ne ya sa amincewar jama’a ta gushe. Har ma mu da muka yi amfani da mutuncinmu wajen bayyana wa mutane al’amura da kuma yin kira mai ƙarfi ga ’yan Najeriya, har zuwa yau ba ni da cikakken bayani kan ainihin abin da ya haddasa wannan matsalar fasaha.”
Igini ya bukaci a dauki darasi a 2027
Sai dai lauyan ya ce zaɓen 2027 zai zama hukunci kan ko ’yan Najeriya za su iya koyon darasi daga abin da ya faru a zaɓen 2023.
“Kowane zaɓe jarrabawa ne, amma zaɓen 2027 zai wuce jarrabawa. Zai zama hukunci kan ko mu a matsayinmu na al’umma za mu iya koyon darasi daga abin da ya faru,” in ji tsohon kwamishinan zaɓen.
Ya buƙaci masu zaɓe a Najeriya da su kasance a ankare, musamman a daren zaɓe lokacin da ake tattara sakamako, domin kare ƙuri’unsu.

Source: Twitter
An maka INEC a gaban kotu
Kun ji cewa SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin INEC da rashin yin cikakken bayani kan sama da N126.46bn.
Ƙungiyar ta nemi kotu ta tilasta wa INEC bayyana yadda aka kashe kuɗin, waɗanda suka amfana da su da kuma kamfanonin da suka karɓi kwangiloli
Asali: Legit.ng
