Hotuna kyawawa
Maimakon ya kera gidansa kamar na kowa, wani mai aikin zanen gida dan Najeriya ya yanke shawarar fita daban a kauyensa. Ya ginawa kansa zagayayyen gida.
Wata attajirar mata yar Najeriya ta ba mahalarta taron da ta shirya na karshen shekara kyautar tukunyar gasa. Ta farantawa mutanen rai ba kadan ba.
Wani mutumin kasar Kenya ya ba da mamaki bayan ya fasa asusun katako da ya shafe tsawon shekara tana tara kudi, wanda hakan ya burge mutane da dama.
A ranar Asabar, 23 ga watan Disamba ne jama'a suka shaida daurin aure tsakanin Mustapha Sani Abacha da kyakkyawar amaryarsa, Safa Tijjani Saleh Geidam.
Yar fafutuka a Najeriya, Aisha Yesufu, ta shawarci yan mata da su furtawa saurayi cewa suna sonsa da zaran sun ji ya kwanta masu ba wai su tsaya jira ba.
Wani bidiyo ya nuno irin bidirin da aka sha bayan wani matashi ya isa kauyensa a cikin motarsa mai budaddiyar mota. Yara da manya sun taru don kallon mamaki.
Wata kyakykyawar daliba ta fashe da kuka bayan wani matashi ya ba ta kyautar naira dubu 20. Dama dai dalibai ta jima tana zullumin yadda za ta biya kudin makarantar.
Shahararren mai watsa shirye-shirye na kasar Ghana, Michael Houston ya yi wuff da kyawawan yan mata biyu a rana daya. Ya ce ya rasa abokai da dama saboda wannan.
Wani bidiyo ya nuno makudan kudi da wani direban tasi ya tsinta a cikin motarsa. An rahoto cewa wani fasinjan Port Harcourt ne ya manta da shi a cikin motar.
Hotuna kyawawa
Samu kari