“Na Shafe Tsawon Watanni Ina Zawarcinsa”, Aisha Yesufu Ta Magantu Kan Yadda Suka Hadu da Mijinta

“Na Shafe Tsawon Watanni Ina Zawarcinsa”, Aisha Yesufu Ta Magantu Kan Yadda Suka Hadu da Mijinta

  • A kwanan nan ne yar fafutuka Aisha Yesufu ta ba yan mata da basu da aure shawara
  • Mai rajjin kare hakkin dan adam din ta bukaci yan mata da su furtawa saurayin da suka ya yi masu so maimakon jira
  • Aisha ta bayyana cewa ita da kanta ta yi zawarcin mijinta bayan ta gan shi a wajen wani biki kuma ta ji ya kwanta mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Yar fafutuka a Najeriya, Aisha Yesufu, ta bayyana yadda ta dauki matakin tunkarar mijinta, Mista Aliu da maganar soyayya.

Matashiyar matar wacce tana cikin wadanda suka kafa tafiyar Bring Back Our Girls ta bayyana cewa sai da ya dauke ta tsawon watanni takwas kafin mijin nata ya amshi tayin soyayyarta bayan ta fada masa yadda take ji game da shi.

Kara karanta wannan

“Na kashe shi ne saboda ya hana ni kashe kaina”: Matar da ake zargi da kashe abokin mijinta a Kano

Aisha Yesufu ta ba da labarin haduwarsu da mijinta
“Na Shafe Tsawon Watanni Ina Zawarcinsa”, Aisha Yesufu Ta Magantu Kan Yadda Suka Hadu da Mijinta Hoto: Buzz Nigeria
Asali: UGC

Misis Yesufu ta bayyana hakan ne a shafinta na X a ranar Asabar yayin da take martani ga bidiyon yadda 'yar wasan motsa jikin Amurka Simone Biles da mijinta, Jonathan Owens suka hadu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce tana da shekaru 23 lokacin shi kuma mijin nata yana da shekaru 35 lokacin da ta yi zawarcinsa.

Idan kun ga wanda ya yi maku ku yi magana, Aisha Yesufu ga yan mata

Ta karfafawa yan mata gwiwar bibiyar namijin da suke mafarkin mallaka maimakon jiran sai shi ya fara furta masu so.

Ta rubuta:

"Na gan shi, na fada tarkon sonsa, sannan na dunga binsa, kuma ya dauki tsawon watanni takwas kafin ya zo, sannan bayan watanni takwas, mun yi aure. Saboda haka gaba daya aikin watanni 16 ne. Daga rnar 13 ga watan Disambar 1996 zuwa ranar 17 ga watan Afrilun 1998."

Kara karanta wannan

Matashi ya tashi kan yan kauye da motarsa mai budaddiyar sama, bidiyon ya yadu

Ta jaddada jin dadin dake tattare da mutum ya yarda cewa matarsa ce ta fara yunkurawa, tare da sauya tsarin al'ada.

Matar mai shekaru 49 ta bayyana cewa ta kan zolayi mijin cewa idan ba don ta yi zawarcinsa ba da yanzu ta rasa abu mai kyau.

Ta bayyana cewa bata taba yarda da cewar dole sai namiji ya fara tunkararta da maganar so ba.

Misis Yesufu ta ce ta gamsu da zama haka ba aure kuma mutane da yawa sun yi mamaki lokacin da ta yi aure, inda ta nuna cewa ana sa ran za ta ci gaba da zama ba aure ba.

Ga bidiyon jawabin nata a kasa:

Bidiyon lefen amaryar dan Sani Abacha

A wani labari na daban, mun ji cewa ana shagulgulan biki a gidan tsohon shugaban kasa, marigayi Sani Abacha inda dansa, Mustapha Sani Abacha ke angwancewa.

A ranar Asabar, 23 ga watan Disamba ne dandazon jama'a suka shaida daurin aure tsakanin Mustapha da kyakkyawar amaryarsa, Safa Tijjani Saleh Geidam a masallacin Mohammed Ali da ke garin Maiduguri, jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel