Matashi Ya Tashi Kan Yan Kauye Da Motarsa Mai Budaddiyar Sama, Bidiyon Ya Yadu

Matashi Ya Tashi Kan Yan Kauye Da Motarsa Mai Budaddiyar Sama, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi ya dauka hankali bayan ya tashi kan mutanen kauyensa da wata mota mai budaddiyar sama
  • Manya da yara daga kauyen sun taru cike da mamaki yayin da suke kallon matashin yana murza motar tasa
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyon sun nuna damuwa cewa wani mummunan abu na iya samun mutumin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A wani bidiyo da ya yadu, wani mutumi ya haddasa cece-kuce bayan ya isa kauyensa a wata mota mai budaddiyar sama.

Yara da manya sun kewaye shi yayin da suke kallo cike da mamaki lokacin da mutumin ke yi kamar bai san yana daukar hankali ba.

Matashi ya ja hankalin mutanen kauyensa
Matashi Ya Tashi Kan Yan Kauye Da Motarsa Mai Budaddiyar Sama, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @mariam_millimono
Asali: TikTok

Wata mai amfani da TikTok, @mariam_millimono, ce ta saki bidiyon, tana mai bayyana cewa ya faru ne a kauye amma bata bayyana ko nata bane.

Kara karanta wannan

Yar Najeriya ta koka bayan ta bude jakar yar aiki a gida, ta ga abubuwan ban mamaki a ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya zauna a cikin motar da yarinya a hannunsa yayin da ya rufe saman motar, lamarin da ya ba mutanen kauyen mamaki.

Bidiyon ya samu masu kallo fiye da 700k a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun nuna damuwa a kansa

Ice-cream ya ce:

"Ba zan iya gwada wannan a karfamin kauyena ba bana son mutuwar wuri."

sekatteratiifu@gmail.com ya ce:

"A kauyena za su fara kiranka kowani taro a matsayin babban bako."

user1441311102127 ya ce:

"Yanzu matan kauyen suna so ya aure su."

Lord Isaac ya ce:

"A kauyena shine hanya mafi sauri da mutum zai bar duniyar nan."

spoiler ya ce:

"A kauyena idan ka yi irin wannan karshen arzikinka kenan, za su lashe ka."

Cypher ya ce:

"Mutanen kauye ba su san cewa a birni ana aron irin wadannan motar ba."

Kara karanta wannan

Waiwayen shekara: Jerin yan siyasar Najeriya mafi shahara a 2023

Kerry~Keruboh ya ce:

"Magana ta gaskiya idan na kai wannan kauyena washe gari zan mutu."

An turawa matashi kudi bisa kuskure

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya mai suna Chim Di Ebere a Facebook, ya sanar da duniya bayan an yi kuskuren tura masa kudi N289,770 a asusun bankinsa.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, mutumin ya wallafa hoton sakon da ya samu da ke nuna kudin da aka tura masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel