“Mutumin Kirki”: Lakcara Ya Taimaki Dalibarsa Mai Jego da Goyon Danta, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

“Mutumin Kirki”: Lakcara Ya Taimaki Dalibarsa Mai Jego da Goyon Danta, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wani lakcara mai kirki a Kwalejin Fasaha ta Gateway, jihar Ogun, ya taimaki daya daga cikin dalibansa daukar danta da ke kuka yayin daukar darasi
  • Ana cikin daukar karatu ne lokacin da yaron ya fara rigima da damu mahaifiyarsa sai lakcaran ya ce ta kawo ya taimaketa da shi
  • Yaron ya yi lamo a bayan lakcaran yayin da shi kuma ya ci gaba da koyar da ajin lamarin da ya burge dalibansa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani lakcara a Kwalejin Fasaha ta Gateway ya sha jinjina a soshiyal midiya saboda soyayyar da ya nunawa daya daga cikin dalibansa.

A cikin wani bidiyo da ya yadu, an nuna cewa daya daga cikin dalibansa mata tana jego kuma yaronta na ta kuka yayin da ake tsaka da daukar darusa a aji.

Kara karanta wannan

Dirama yayin da yayar amarya ta hana wata yi mata liki a wajen biki, bidiyon ya haddasa cece-kuce

Lakcara dauke da goyo a aji
“Mutumin Kirki”: Lakcara Ya Taimaki Dalibarsa Mai Jego da Goyon Danta, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: TikTok/@oreke2608.
Asali: TikTok

Domin taimaka ma dalibar tasa, lakcaran ya karbi jinjirin daga hannun mahaifiyarsa domin ta samu damar mayar da hankali kan karatun da ake yi a aji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano lakcaran mai suna Dr Adekunle goye da jinjirin a bayansa. Mutane da dama da suka ga bidiyon sun yaba ma lakcaran.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da lakcara ya yi goyo

@Tiwalade571 ta ce:

"Dr Adekunle da a kullun yake yi mana addu'o'i yayin daukar darasi da lokutan jarrabawa ina tsananin kaunar mutumin nan. Allah ya albarkaci gidanka"

@Ayoni~Mofe ta ce:

"Akwai dalibin TASUED a nan. Ku tayani ambaton sunan Awofodu. Ya ga lakcara dan uwansa."

@adunola ta ce:

"Ku taya ni ambatan sunan wani lakcaran kwalejin Kwara don Allah."

@iraj Thrift ta yi martani:

"Babu wani lakcara da zai iya yin wannan a Laspotech."

Kara karanta wannan

"Na wahala da shi": Budurwa ta fashe da kuka yayin da saurayinta na shekaru 7 ya auri wata

@ifunanya chukwu ta ce:

"Don Allah Fuoye ku tayani ambatan sunan amazuma don ya ga takwaransa."

@olaronkekaka ta ce:

"Lakcara da ke da faran-faran."

Malami ya dauki jinjirin dalibarsa

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wani lakcara da ba a san daga wani makaranta yake ba ya sha ruwan yabo da jinjina bayan wani bidiyonsa ya yadu a TikTok.

A wani bidiyo da ya yadu wanda @Olashile75 ya wallafa, an gano malamin dauke da jinjirin daya daga cikin dalibansa mata cike da farin cikin ganinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel